Daga JOHN D WADA a Lafia
Shugabannin ƙabilar Migili a Jihar Nasarawa sun roƙi gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule da ya zaɓi ɗan asalin Migili a matsayin mataimakin wanda zai gaje shi a zaɓen 2027.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Lafia ranar Litinin, kwamared Sunday Aleku, mai magana da yawun matasan ƙungiyar masu ruwa da tsaki na Migili yace rokon yana da nufin tabbatar da cewa an ji muryar ƙungiyar a matakin mulki mafi girma na jihar.
A cewar Aleku, mutanen Migili sun kasance masu goyon baya ga gwamnatoci daban-daban da daɗewa kuma suna taka rawar gani wajen cigaban siyasa a jihar ta Nasarawa baki ɗaya. Yace wannan tarihin ya isa ya basu damar a yi la’akari da su domin muƙamin mataimakin gwamna.
Ya bayyana cewa al’ummar Migili na yaɗuwa a ƙananan hukumomin Lafia da Obi da Awe da Keana da Karu da kuma suna da yawan masu jefa ƙuri’a da ya wuce 120,000.
Ya cigaba da bayyana cewa “Ko da yake mun kasance masu aminci masu sadaukarwa kuma da masu ba da gudummawa.
Al’ummar Migili ba ta taɓa samun gwamna ko mataimakin gwamna ba tun bayan kafa Jihar Nasarawa,” inji Aleku.
Ya kara da cewa gyara wannan rashin daidaito yana da muhimmanci domin tabbatar da adalci da shugabanci na haɗin kai.
Ƙungiyar ta kuma roƙi gwamna Sule da Sanata Ahmed Aliyu Wadada wanda gwamnan ya zaɓa a matsayin ɗan takarar APC na 2027 da kuma shugabancin jam’iyyar APC gaba ɗaya da su mara wa ɗan takara mai cancanta daga Migili baya domin muƙamin mataimakin gwamna.
Masu ruwa da tsakin sun kuma bada shawarar Honarabul Sonny Agassi a matsayin wanda ya cancanta da muƙamin daga cikin al’ummar ƙabilar Migillin nasu inda suka ambaci ƙarfinsa a matakin al’umma da sadaukarwarsa ga APC.
Aleku a ƙarshe sai ya jaddada cewa wannan buƙata ba ta samo asali daga ra’ayin ƙabilanci ko kawo rarrabuwa ba sai dai sha’awar samun daidaito da wakilcin dukkan al’ummomi a tsarin shugabancin jihar ne.
