DCP Ahmed ya kada Sanata Goje a zaɓen fidda gwanin APC na Gombe ta Tsakiya

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI GOMBE Gombe

Ɗaya daga cikin masu neman takarar kujerar Sanatan Gombe ta tsakiya a ƙarƙashin jam’iyyar APC, DCP Ahmed Muhammad (mai ritaya), ya bayyana ƙwarin gwiwarsa na lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar, bayan yadda ya ce an gudanar da zaɓe cikin lumana a ƙaramar hukumar Yamaltu-Deba.

Da yake zantawa da manema labarai a Deba bayan sa ido kan yadda zaɓen ke gudana, tsohon mataimakin kwamishinan ’yan sanda ya ce an gudanar da aikin cikin tsari, natsuwa da bin doka ba tare da wata tangarda ba.

Ya ce hakan na daga cikin alamun sauyin ra’ayi da ake samu a siyasar yankin.

“Abin da muka gani a Yamaltu-Deba ya kasance cikin lumana da kwanciyar hankali. Komai ya gudana cikin tsari ba tare da wata matsala ba,” in ji shi.

DCP Ahmed, wanda ke ƙalubalantar Sanata Goje bayan shafe shekaru 16 yana wakiltar mazaɓar a Majalisar Dattawa, ya ce sakamakon da ake gani na nuna yadda jama’a ke ƙara neman sabuwar hanya a wakilcin Gombe ta tsakiya.

Ya ƙara da cewa jama’a da mambobin jam’iyya sun nuna gamsuwa da bukatar sabuwar jagoranci mai ƙarfi da zai kawo ci gaba mai ɗorewa ga yankin.

“Kowa na ganin farin cikin jama’a. Mutane da dama na ganin lokaci ya yi da Yamaltu-Deba za ta samu wakilci mai ƙarfi a matakin ƙasa,” in ji shi.

A ƙarshe, ya jaddada cewa burinsa ba wai hana kowa takara ba ne, sai dai amsa kiran jama’a na neman sabon salo da sabuwar alkibla a shugabancin yankin.

By ukarofi