
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An amince da dukkan sharuɗɗa tsakanin José Mourinh da ƙungiyar Real Madrid domin sanannen kocin ya koma horar da ‘yan wasanta.
Yanzu abin da ya rage shi ne sanya hannun akan takardu, wanda za a yi a wannan watan.
Shirin yarjejeniyar farko ta shekaru biyu da Mourinho bai haifar da wata matsala ba domin burinsa kawai shine komawa Real Madrid, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Haka kuma, Mourinho mai shekaru 63 zai je Madrid bayan wasanta da Atletico Bilbao, tare da shirin fara sabon babi a Bernabéu, kamar yadda ƙwararren ɗan jaridar akan harkar wasanni, Fabrizio Romano ya bayyana.
