Batun hana iyalan El-Rufa’i ganawa da shi ba gaskiya ba ne, inji ICPC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Yaƙi da Rashawa ICPC, ta musanta zarge-zargen da ake mata cewa ta hana a gana da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i a lokacin da yake tsare a hannunta.

El-Rufa’i ya zauna a hannun ICPC tun daga ranar 19 ga watan Fabarairu bisa zargin sa da sauya akalar wasu maƙudan kuɗaɗe a lokacin da yake gwamnan Kaduna daga shekarar 2015 zuwa 2023.

A Rane 13 ga watan Afrilu, hukumar ta gurfanar da tsohon gwamnan a Babbar Kotun Kaduna bisa tuhumarsa da hannu a laifuka 9 masu alaƙa da badaƙalar da wulaƙanta ofis.

Al’amarin ya faɗaɗa ne a lokacin da Ɗan Majalisar Wakilai kuma ɗan El-Rufa’i, Mohammed Bello da ke wakiltar mazaɓar Kaduna ta Arewa ya zargi ICPC da hana matar mahaifinsa kai wa mijinta abinci.

Haka kuma, ya zargi jami’an hukumar da hana wani likita ganin mahaifin nasa, yana mai bayyana hakan a matsayin saɓa wa ‘yancin ɗan-adam na tsohon gwamnan.

Saidai, da yake ganawa da manema labarai, Kakakin ICPC, Okor Odey ya yi watsi da zarge-zargen inda ya bayyana su a matsayin ƙarya da ake ƙoƙarin ruɗar da al’umma da su.

A cewarsa, hukumar ta nuna damuwa akan yadda mutane ke ƙirƙirar ƙarya akanta.

Ya ce, ICPC ta ba baƙi damar zuwa ziyara a kullum daga ƙarfe 9 na safe zuwa 6:30 na yamma. Ya bayyana cewa matar El-Rufa’in ta je ne ba a lokacin da aka amince wa baƙi halarta ba.

Ya ƙara da cewa, za a iya duba takardar rajistar sunayen iyalai da dalilansu na halarta domin tantance haƙiƙanin abin da ya faɗa.

By Babaji