
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne, sun halaka kimanin sojoji guda bakwai tare da wani farar hula ɗaya yayin wani harin kwanton-ɓauna a ƙauyen Runji da ke Ƙaramar Hukumar Illela a Jihar Sakkwato.
Majiyoyi sun ce harin ya faru ne yayin da jami’an tsaron ke sintiri a yankin da ke kusa da iyakar Nijeriya da Nijar, inda maharan suka buɗe musu wuta a halin ba-zata.
Sun bayyana cewa an yi musayar wuta mai tsanani tsakanin sojojin da maharan kafin lamarin ya lafa, yayin da aka ce an kai waɗanda suka jikkata asibiti domin samun kulawa.
Haka kuma, wata majiya ta ce sojojin sun kai wa ‘yan ta’addan hari ne tare da lallasa su a wani sansani gabanin kwanton-ɓaunar.
Har zuwa yanzu hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan harin ba, amma ana ci gaba da gudanar da bincike da kuma farautar maharan a yankin.
