
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An kwantar da tsohon Maitaimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar a asibiti sakamakon fama da rashin lafiya da ya same shi a ƙarshen makon da ya gabata, lamarin da ya sa aka ɗage taron tantance ‘yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar adawa ta ADC.
Akan haka ne wasu majiyoyi suka ce likitoci sun umarce shi da ya huta a gadon jinya na wani ɗan lokaci domin samun sauƙi daga halin da ya shiga.
Sun ce wannan ne ya janyo dage tantancewar ’yan takarar neman tikitin shugabancin ƙasa na jam’iyyar da aka shirya gudanarwa a kwanan nan.
Saidai har yanzu jam’iyyar ba ta fitar da cikakken bayani a hukumance ba akan halin da ake ciki game da al’amarin.
Rashin lafiyar tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya sa wasu shirye-shiryen siyasa da ya kamata ya halarta suka samu tangarɗa, yayin da magoya baya da ’yan siyasa ke cigaba da jiran sahihin bayani daga ɓangarensa da kuma ADC.
A halin yanzu, ana cigaba da tattaunawa a fagen siyasa akan tasirin wannan jinkiri, musamman ganin yadda zaɓen 2027 ke ƙara kusantowa.
