Da ma siyasar Nijeriya ta Musulmai ce kaɗai?

Spread the love

Daga UNCLE LARABI

Tambayar da ke bakina ita ce, da ma siyasar Nijeriya ta Musulmai ce kaɗai ko kuma dole sai wanda zai yaudare ku da son musulunci za ku zaɓa? Mutane suna ba ni mamaki akan Peter Obi wai ba ya son Musulunci. Yanzu ba kakanku, Musulmin ke mulki ba Omologo? Uban me ya tsinana muku na kasancewarsa Musulmin banda azaba da yake gana mana?

To, bari ku ji. Yanzu na ƙara hankali, na ƙara ilimi, na ƙara wayo, idona ya buɗe. Nigeria ba ta Musulmi ba ce, bare Musulmin bogi. Don haka ba Peter Obi ba, wallahi ko Ojuku ne zai dawo duniya, idan har zai tsaya takata kuma ya yi sanadin kawar da wannan gwamnatin ta APC da Omologo, wallahi zan zaɓe shi. 

Haba! Yanzu fa mu masu motar hawa sai mutum ya shirya, sai dole sai kuma mara lissafi ko wanda yake ci a gwamnati ko wani wajen da kuɗi ke shigowa ba wahala. Idan ba haka ba, ba k yai aune ba a wata sai ka sha man fetur na Naira 250,000. Ina dalili? Siminti fa ya haura Naira 12,000. Yanzu a haka talaka zai yi gini ya yi aure? Ya ƙara nesanta talaka da mallakar mota da gida. Hayar ita kanta wahala da tsada. 

Don haka mutane marasa tunani sai musu, suna nan suna ƙaryar Peter Obi ba ya son Musulunci, ba za su zaɓe shi ba, gara Tinubu ya maimaita… bula-bula! To, a haka za ku ƙara zaluntar kanku.

Ni dai addu’ata duk juyi ita ce, Allah ya ba mu sannan kuma kada ya sa mu rasa abin da za mu biya wa kanmu buƙata. Allah ya yauƙaƙa jarinmu. 

Dan uwanku. ƙaninku, abokinku, Abdullahi Jibril Larabi (Uncle Larabi); 08065418892, Jihar Kano – Nijeriya

9 ga Mayu, 2026

By ukarofi