APC na lallashi na bayan faɗuwa a zaɓen fidda gwani, inji Cubana Cif Priest

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanannen hamshaƙin ɗan kasuwa daga kudancin Nijeriya da ake kira da Cubana Chiefpriest ya haddasa cece-kuce a kafafen sada zumunta sakamakon cewa an ba shi kyautar dalleliyar mota bayan faɗuwarsa a zaɓe.

Da yake jawabin a wata hira da Peller ya jagoranta, Cubana Chiefpriest ya ce duk da cewa wasu na sukar sa, mambobin jam’iyyar APC na cigaba da taimaka masa da kuma ƙarfafa masa gwiwa a halin rashin nasarar da ya samu.

A cewarsa, wani daga cikin shugabannin APC ya kai masa ziyara bayan zaɓen, inda ya faɗa masa cewa an saya masa sabuwar mota domin lallashin sa.

Ya ƙara da cewa, shi da ‘yan tawagarsa za su ɗauko motar a washe gari, yana mai iƙirarin cewa yana da abokai masu tasiri sosai acikin tafiyar da harkokin siyasarsa.

By Babaji