Ya rasu ba shi da ɗa bayan sama da shekara 10 da aure, inji iyalan malamin da aka wa kisan gilla a Oyo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Iyalan marigayi Michael Oyedokun, wato malamin makarantar nan da ‘yan bindiga suka yi wa kisan gilla a Jihar Oyo, sun bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi a gare su, inda suka ce ya rasu ne ba tare da haihuwa ko ɗaya ba duk da cewa aurensa ya haura shekara goma.

Oyedokun na ɗaya daga cikin malaman da ‘yan bindiga suka sace a wasu makarantu da ke Ƙaramar Hukumar Oriire a Jihar Oyo.

An yi awon-gaba da marigayin ne tare da wasu abokan aikinsa daga makarantar Community High School, da ke Ahoro-Esiele yayin harin na ranar Juma’a.

Sauran makarantun da ‘yan bindigar suka kai farmaki sun haɗa da Baptist Nursery and Primary School, Yawota, da kuma LA Primary School na garin Ogbomoso.

A sakamakon haka ne gwamnatin jihar ta umarci a rufe makarantu a ƙananan hukumomi guda huɗu yayin da jami’an tsaro suka duƙufa wajen ceto mutanen da aka sace.

Haka kuma, an ga yadda bidiyon kisan gillar ya karaɗe kafafen sada zumunta, inda a ciki aka tilasta wa marigayin yin magana gabanin halaka shi, lamarin da ya haddasa cece-kuce da fargaba akan makomar sauran waɗanda ke hannun maharan.

Wani mai suna Ebeni Adediran da ya magantu a madadin iyalan marigayin, ya shaida wa ShaharaReporters cewa Oyedokun ya kasance mutum ne mai son zaman lafiya da girmama mutane wanda ya sadaukar da rayuwarsa na tsawon sama da shekaru 20 yana karantarwa.

By Babaji