Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Farfesa Segun Aina a matsayin sabon magatakardan Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta ƙasa (JAMB), inda zai gaji Farfesa Is-haƙ Oloyede wanda wa’adinsa na zangon mulki na biyu zai ƙare a ranar 31 ga Yuli, 2026.
Farfesa Aina, wanda zai cika shekaru 40 a watan Yulin 2026, fitaccen masani ne a fannin ilimi da tsarin fasaha, tare da gogewa mai yawa kan tsarin gudanar da jarabawar ƙasa, fasahar zamani da gyaran hukumomin gwamnati.
Ya yi digirin farko na Bachelor of Engineering a fannin Computer Systems Engineering daga Jami’ar Kent, sannan ya samu digirin MSc a fannin Internet Computing and Network Security da kuma PhD a Digital Signal Processing daga Jami’ar Loughborough da ke Birtaniya.
Haka kuma ya kammala shirin horaswa na manyan jami’an gudanarwa a Lagos Business School.
A matsayinsa na Farfesa a fannin Computer Engineering a Jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife, Aina ya fara aiki da JAMB tun lokacin bautar ƙasa (NYSC), inda ya samu gogewa kan tsarin shiga jami’o’i da tsarin sarrafa bayanai.
An bayyana cewa wannan gogewa ce ta taimaka masa wajen bayar da gudunmawa a gyaran tsarin jarabawa da inganta hanyoyin gudanarwa ta amfani da fasaha.
Tare da fiye da shekaru 15 na gogewa bayan kammala karatu, Farfesa Aina ya yi fice wajen haɗa fasaha, manufofi da sauya tsarin hukumomi, inda yake ba gwamnatocin tarayya da jihohi shawara kan tsarin gudanarwa, sauya tsarin zuwa na zamani da kuma gyaran ayyukan hukumomi.
Yana da shekaru 39 lokacin da ya zama ɗaya daga cikin mafi ƙarancin shekaru da suka zama farfesa a fannin Computer Engineering a Nijeriya, kuma yanzu zai kafa tarihi a matsayin mafi ƙarancin shekaru da ya zama magatakardan JAMB.
Ya kuma yi aiki a matsayin mai ba da shawara ga manyan hukumomin jarabawa kamar NECO, NABTEB da wasu ma’aikatun ilimi na jihohi, inda yake bayar da ƙwarewa kan tsarin ICT, kare ingancin jarabawa da inganta hanyoyin gudanar da aiki ta amfani da fasaha.
Farfesa Aina mamba ne a ƙungiyoyi masu zaman kansu da dama, ciki har da Council for the Regulation of Engineering in Nigeria (COREN), Nigerian Society of Engineers (NSE), Institute of Electrical and Electronics Engineers (IEEE) da Institution of Engineering and Technology (IET).
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa yana sa ran Farfesa Aina zai yi amfani da gogewarsa, iliminsa da fahimtarsa wajen ci gaba da ɗaga martabar JAMB fiye da irin nasarorin da wanda ya gada ya samu.
