Tinubu ya umarci hukumomin gwamnati su rungumi tsarin aiki da fasahar zamani

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa zamanin tafiyar da aikin gwamnati cikin jinkiri da dogaro da takardu na hannu ya kamata ya zama tarihi, yana mai jaddada cewa dole ne Nijeriya ta rungumi tsarin aiki mai sauri, gaskiya da amfani da fasahar zamani wajen gudanar da mulki.

Saboda haka, shugaban ƙasar ya umarci dukkan Ma’aikatu, Sassa da Hukumomin Gwamnati (MDAs) da su ƙara zurfafa amfani da tsarin dijital a dukkan harkokin gudanar da ayyukansu.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da Taron ƙasa da ƙasa kan Aikin Gwamnati na 2026 da aka gudanar a Abuja, inda ya ce sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayya ta fara sun fara haifar da sakamako mai ma’ana, tare da bayyana cewa ma’aikatu da hukumomi 38 sun riga sun koma tsarin aiki na zamani mara amfani da takardu.

Yayin da yake jawabi ga mahalarta taron daga ƙasashen Afirka da sauran sassan duniya, shugaban ya ce sauya fasalin aikin gwamnati na daga cikin ginshiƙan ajandar gwamnatin sa ta “Renewed Hope Agenda”, yana mai cewa babu wata manufa ta gwamnati da za ta yi nasara ba tare da ingantaccen aikin gwamnati ba.

“Lokacin jinkirin aikin hannu ya ƙare. Dole ne mu rungumi aiki cikin sauri, gaskiya, yanke hukunci bisa bayanai da kuma bayar da sabis da ke mayar da hankali kan buƙatun jama’a,” inji Tinubu.

Shugaban ya bayyana cewa taken taron na bana mai taken “Sauye-Sauye, Juriya da Sakamako” ya nuna yadda Nijeriya ke sauyawa daga manufofi kawai zuwa aiwatar da su tare da samun sakamako a zahiri.

A cewarsa, aikin gwamnati a Nijeriya ya nuna ƙwarewa da juriya cikin watanni 11 da suka gabata duk da matsin tattalin arzikin duniya da kuma ƙarin buƙatun cikin gida.

“Ku ne injin sauya ƙasa. Yanzu wannan injin yana zama mai sauri, mai basira, mai gaskiya da kuma mai saurin amsa buƙatun jama’a,” shugaban ya shaida wa ma’aikatan gwamnati da abokan hulɗar ci gaba.

Tinubu ya ce, lokacin da gwamnatinsa ta fara matsa kaimi kan tsarin dijital a shekarar 2025, mutane da dama sun ɗauka a matsayin buri na dogon lokaci, amma yanzu ana ganin sauye-sauyen a aikace.

Ya ce, an tsara tsarin dijital ne domin inganta ayyukan gwamnati, jawo hannun jari, ƙarfafa ƙirƙire-ƙirƙire da kuma bunƙasa tattalin arziki mai anfani ga kowa.

Shugaban ya kuma danganta sauye-sauyen aikin gwamnati da babban shirin gwamnatin tarayya na bunƙasa fasahar dijital mai suna “Project BRIDGE”, wato gina ingantaccen tsarin fasahar sadarwa domin ci gaban ƙasa.

Tinubu ya tuna da tattaunawar da aka yi a taron “Africa CEO Forum” da aka gudanar a Rwanda, inda ya ce Nijeriya na ƙoƙarin zama cibiyar zuba jari a harkar fasahar dijital a Afirka.

“A yayin da muke ƙara hanzarta tafiyar sauya fasalin dijital, muna maraba da masu zuba jari da abokan hulɗa domin shiga cikin tsarin fasahar Nijeriya,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa hukumomin gwamnati dole su rungumi fasahar zamani ba kawai a gudanar da ayyukan ofis ba, har ma wajen bayar da sabis ga jama’a.

Tinubu ya kuma bayyana cewa aikin tantance ma’aikata da binciken giɓin ƙwarewa da aka fara a taron shekarar 2025 na daf da kammala, wanda zai taimaka wajen gano giɓin ƙwarewa da kuma sanya ma’aikata a inda suka dace.

“Muna gano giɓin ƙwarewa, muna ƙarfafa basira, tare da tabbatar da cewa an sanya mutanen da suka dace a wuraren da suka dace,” inji shugaban.

Ya kuma jaddada cewa ana aiwatar da waɗannan sauye-sauye ne domin bai wa ma’aikatan gwamnati ƙwarewar dijital da ɗabi’ar aiki da ta dace da ƙarni na 21.

By ukarofi