Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD
A wata shari’a mai cike da zarge-zarge a Babban Kotun Tarayya da ke Abuja, wani wanda ake tuhuma da hannu a shirin juyin mulki ya bayyana yadda ake zargin wasu suka shirya kutsawa Fadar Shugaban ƙasa ta hanyar amfani da ƙofar shigar motocin gaggawa, wato ambulance entrance, a wani ɓangare na abin da ake zargi da yunƙurin kifar da gwamnati.
Wannan bayani ya fito ne a zaman kotu na ranar Laraba a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, inda aka gabatar da shaidar bidiyo da ke da alaƙa da ɗaya daga cikin waɗanda ake tuhuma, Zekeri Umoru.
Umoru, wanda ma’aikaci ne na kamfanin Julius Berger Nigeria a sashen gyaran Fadar Shugaban ƙasa, ya shaida wa kotu cewa a cikin tattaunawar da ake zargin an yi, har da shirin yanke wutar lantarki a cikin fadar domin sauƙaƙa aiwatar da abin da ake zargin.
A cewarsa, wanda ake zargin jagoran shirin, Kanal Mohammed Ma’aji, ya tunkare shi ta hannun wani ɗan sanda, Sufeto Ahmed Ibrahim (wanda shi ne wanda ake tuhuma na uku), inda aka ba shi tayin kuɗi domin ya tattara mutane 18 zuwa 19 daga cikin ma’aikatan da ke aiki a cikin fadar.
Ya bayyana cewa waɗanda ake son jawowa cikin shirin sun haɗa da sojoji, jami’an Hukumar Tsaro ma Farin Kaya (DSS) da kuma ma’aikatan Julius Berger da ke aiki a cikin rukunin fadar shugaban ƙasa.
Umoru ya ƙara da cewa, daga baya Sufeto Ahmed Ibrahim ya nemi a ba shi Naira miliyan 100 daga hannun Ma’aji domin buɗe hanya ta amfani da ƙofar motocin gaggawa domin shiga Aso Rock.
Sai dai ya ce, Ma’aji ya ƙi amincewa da wannan kuɗi, yana mai cewa ya yi yawa, inda ya yi iƙirarin cewa zai iya shiga fadar “da ƙarfi” idan waɗanda aka shirya ciki suka ƙi haɗin kai.
Umoru ya ce, daga baya ya fara jin tsoro da rashin jin daɗi game da shirin, har ma ya yi ƙoƙarin mayar da kuɗin da aka ba shi.
Ya bayyana cewa daga ƙarshe ya fahimci cewa shiga Fadar Shugaban ƙasa “ba abin wasa ba ne.”
Ya kuma musanta zargin cewa yana da damar shiga rukunin makamashin hasken rana na fadar ko kuma yana da hannu wajen yanke wutar lantarki a cikin babban fadar gwamnati.
A cewarsa, dalilin da ya sa bai kai rahoton lamarin ga hukumomin tsaro nan take ba shi ne saboda Sufeto Ibrahim ya hana shi yin hakan.
Bayan zaman kotu, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta ɗage shari’ar zuwa ranar 21 ga Mayu domin ci gaba da sauraron shari’ar binciken farko (trial-within-trial), wadda ke nufin tantance ko bayanan da waɗanda ake tuhuma suka bayar na son rai ne ko akasin haka.
Gwamnatin Tarayya, ta hannun Ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a (AGF), ta gurfanar da waɗanda ake tuhuma kan tuhume-tuhume 13 da suka shafi laifin cin amanar ƙasa, ta’addanci, rashin kai rahoton bayanan tsaro, da kuma badaƙalar kuɗaɗe da ake zargin suna da alaƙa da tallafin ta’addanci.
Lamarin ya ci gaba da janyo hankalin jama’a, lauyoyi da masana tsaro, yayin da kotu ke ci gaba da tantance sahihancin zarge-zargen da ake gabatarwa.
