Michael Carrick ya amince da zama kocin Manchester United na shekara biyu

Spread the love

Ƙungiyar Manchester United ta sanar da naɗin Michael Carrick a matsayin kocinta ‘yan wasanta na dindindin, inda zai cigaba da jagorantar ta har zuwa shekarar 2028.

Carrick, wanda tsohon ɗan wasan United ne, ya samu wannan muƙamin ne bayan rawar gani da ya taka a matsayin kocin wucin gadi tun daga watan Janairun 2026.

A ƙarƙashin jagorancinsa, United ta samu sauye-sauye masu kyau, ciki har da samun gurbin shiga Gasar Zakarun Turai (Champions League) da kuma kammala kakar Premier League a matsayi na uku.

Rahotanni sun bayyana cewa, shugabannin ƙungiyar sun gamsu da irin tasirin da Carrick ya yi akan ‘yan wasa da kuma yadda ya dawo da ƙwarin-gwiwar ƙungiyar, wanda hakan ya sa aka amince masa cigaba da aikin a matsayin shugaban koci na dindindin.

Carrick ya bayyana farin cikinsa da wannan sabon matsayi, yana mai cewa zai yi aiki tukuru domin ganin Manchester United ta sake komawa cikin sahun manyan kungiyoyi a Ingila da Turai.

By Babaji