Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta bayyana cewa kamfanonin sadarwa sun zuba sama da dala biliyan ɗaya wajen faɗaɗa hanyoyin sadarwa da inganta ayyukan intanet a faɗin ƙasar nan cikin shekarar 2025 kaɗai.
Shugaban Hukumar NCC kuma Babban Daraktan Gudanarwa, Dakta Aminu Maida, ne ya bayyana hakan a birnin Legas yayin wani taro da Hukumar NCC ta shirya tare da Cibiyar Horas da Alƙalai ta ƙasa domin horas da alƙalai kan harkokin sadarwa da fasahar zamani.
A cewarsa, kamfanonin sadarwar sun ƙara dubban sabbin cibiyoyin sadarwa domin faɗaɗa kewayon intanet da kuma inganta ingancin ayyukan sadarwa a ƙasar.
Ya ce hakan ya nuna juriyar ɓangaren sadarwa tare da muhimmiyar rawar da yake takawa wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya da haɗin kan al’umma.
Dakta Aminu Maida, wanda Kwamishiniyar Hulɗa da Masu Ruwa da Tsaki ta Hukumar NCC, Hajiya Rimini Makama, ta wakilta, ya ce bunƙasar biyan kuɗi ta yanar gizo, kasuwancin intanet, kamfanonin fasaha masu tasowa, ilimin zamani da kuma amfani da sabbin fasahohi na nuna irin damar da tattalin arzikin dijital ke da ita wajen samar da ci gaba da ƙarin damammaki.
Ya bayyana cewa ’yan Nijeriya na amfani da bayanan intanet fiye da kowane lokaci. A cewarsa, a watan Maris na shekarar 2026 kaɗai, ’yan Nijeriya sun yi amfani da sama da terabyte miliyan 1.42 na bayanan intanet, idan aka kwatanta da terabyte dubu 995 da aka yi amfani da su a watan Maris na shekarar 2025. Ya ce hakan na nufin ana amfani da kusan terabyte 45,800 na bayanan intanet a kowace rana.
Dakta Maida ya ƙara da cewa wannan amfani da bayanai ya yi daidai da kallon sama da sa’o’i miliyan 15 na bidiyon HD a kullum daga ’yan Nijeriya. Ya ce idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, ana amfani da ƙarin sa’o’i miliyan 4.6 na bidiyon HD a kullum.
Haka zalika, ya bayyana cewa samun damar amfani da intanet mai sauri na ci gaba da ƙaruwa a ƙasar, inda yawan masu amfani da broadband ya tashi daga kashi 47.70 cikin ɗari a bara zuwa kashi 54.30 cikin ɗari a bana.
A cewarsa, wannan na nuna cewa ƙarin ’yan Nijeriya na samun damar amfani da ingantaccen intanet mai sauri a sassa daban-daban na ƙasar.
