Daga AISHA ASAS
MOPPAN ta bayyana cikakken goyon bayanta ga matakin da Hukumar Tace Fina-finai ta Kano ta ɗauka na dakatar da wasu jaruman Kannywood na tsawon shekara guda, tana mai cewa hukuncin ya dace da abin da suka aikata.
A cikin wata sanarwa ta musamman da shugaban ƙungiyar na ƙasa Shehu Hassan Kano ya fitar, ƙungiyar ta nuna rashin jin daɗinta tare da yin Allah wadai da halayen da suka janyo ɗaukar matakin, tana mai bayyana cewa irin waɗannan ɗabi’u ba su dace da kyawawan halayen Hausawa da kuma koyarwar addinin Musulunci ba.
Sanarwar ta bayyana cewa, abin da aka aikata ya yi karo da tarbiyya, al’ada da kuma ɗabi’un Bahaushe, lamarin da ya sanya ƙungiyar ke ganin matakin da aka ɗauka ya kasance mai dacewa domin kare martabar Masana’antar Kannywood da kuma tsaftace sana’ar daga duk wani abu da zai iya ɓata mata suna a idon al’umma.
ƙungiyar ta ƙara da cewa, tana tare da shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Kano Abba Almustapha, tare da tabbatar masa da cikakken goyon baya da kuma ƙarfafa masa gwiwa wajen gudanar da aikinsa.
A cewar sanarwar, shugabannin MOPPAN sun yi imanin cewa manufar hukumar a kullum ita ce tabbatar da cigaban masana’antar Kannywood tare da kare mutuncinta da martabarta a idon duniya.
Haka kuma ƙungiyar ta yi kira ga ɗaukacin masu ruwa da tsaki a masana’antar, musamman jarumai, furodusoshi da sauran ma’aikatan fina-finai, da su haɗa kai wajen tabbatar da cigaban sana’ar cikin tsari, mutunta al’ada da kuma bin dokokin da aka kafa.
Sanarwar wadda Shehu Hassan Kano ya sanya wa hannu, ta jaddada cewa haɗin kai da bin doka su ne ginshikin ɗorewar masana’antar Kannywood da kuma samun ci gaba mai anfani ga kowa.
