Daga AISHA ASAS
Seyi Tinubu ya aike wa fitaccen ɗan kasuwa kuma jigo a harkar nishadi Cubana Chief Priest saƙon ƙarfafa gwiwa bayan ya gaza samun tikitin Jam’iyyar All Progressives Congress domin tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya daga mazabar Orsu/Orlu/Oru East da ke Jihar Imo.
An gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC ne a ranar Asabar a wani ɓangare na shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027, inda ‘yan takara daga sassa daban-daban suka fafata domin neman amincewar jam’iyya.
Cubana Chief Priest, wanda ke matsayin mai kula da tafiyar ƙungiyar City Boy Moɓement a Jihar Imo, ya shiga takarar ne bayan sayen fom din tsayawa takara da kuma nuna sha’awa.
A baya, ya bayyana cewa manufarsa ita ce bunƙasa rayuwar matasa, kawo ci gaba a yankunan karkara da kuma ƙara yawan matasan da ke shiga harkokin siyasa a mazaɓarsa.
Sai dai duk da shahararsa da kuma goyon bayan da wasu matasa suka nuna masa, hakan bai wadatar ba wajen tabbatar masa da nasara a zaɓen fidda gwanin jam’iyyar.
Bayan bayyana sakamakon zaɓen, Seyi Tinubu wanda shi ne babban jagoran ƙungiyar City Boy Moɓement, ya wallafa saƙo a shafinsa na Instagram domin ƙarfafa masa gwiwa tare da nuna cewa shan kaye a wani mataki ba yana nufin kawo ƙarshen tafiya ba ne.
A cikin saƙon, ya bayyana cewa wani lokaci rashin nasara a wata fafatawa kan zama wata sabuwar hanya ta kaiwa ga babban nasara a gaba.
Ya kuma buƙace shi da ya ci gaba da daga kai tare da nuna ƙwarin gwiwa, yana mai cewa suna sane da irin abubuwan da zai iya cimmawa a nan gaba.
Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, musamman ganin yadda shahararrun mutane daga ɓangaren nishadi ke ci gaba da shiga siyasa gabanin zaɓen 2027, abin da wasu ke ganin wata alama ce ta yadda matasa ke ƙara nuna sha’awar shiga shugabanci da tafiyar da harkokin gwamnati a Najeriya.
