
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jarumar masana’antar Kannywood, Wasila Isma’il ta rasu tana da shekara 46 a duniya bayan fama da wani rashin lafiya na tsawon lokaci.
Tsohon mijinta kuma tsohon aditan jaridar LEADERSHIP Hausa, Al-Amin Chiroma ne ya tabbatar da rasuwarta a wani saƙon Soshiyal Mediya a yammacin ranar Lahadi.
“Innalillahi Wainna Ilaihirrajiun. Wasila Isma’il is dead. She died at the Federation of Muslim Women Associations of Nigeria Hospital, Kaduna,” kamar yadda ya wallafa.
A cewarsa, jarumar ta rasu ne a ranar Lahadi bayan fama da wani dogon rashin lafiya. Ta rayu ne tare da ‘ya’yanta.
Ana ɗaukar marigayiyar a matsayin ɗaya daga fitattun jaruman Kannywood musamman ganin yadda ta haska a finafinai da dama.
A shekarar 1998 ne jarumar ta shiga harkar fim da wani fim mai suna “Jinin Masoya”, amma kuma da shirin “Wasila” da Yakubu Lere ya bayar da umarni inda ta fito tare da jarumi Ali Nuhu aka fi sanin ta.
Jarumar, wadda haifaffiyar Kaduna ce, ta yi shura da sunan fim ɗin, wanda kuma shi ne ainihin sunansa.
A wata hira da aka yi da ita, ta ce da fari an so sanya wa fim suna “Jamila”, kana daga bisani ta nemi a sauya shi zuwa Wasila.
Tuni dai masoya da abokan aiki suka yi ta aika saƙonnin ainihin rashin jarumar, wadda za a jima ana tuna gagarumar gudunmawar da bayar a harkokin masana’antar fim musamman a arewacin Nijeriya.
