‘Yan sanda sun kama tsohon hadimin gwamna Raɗɗa kan zargin sace yaro a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Tsohon hadimin gwamnan Katsina na daga cikin mutane shida da aka kama bisa zargin yin garkuwa da wani ƙaramin yaro mai shekaru takwas inda aka nemi kuɗin fansa daga wajen mahaifansa Naira miliyan 17.

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama Nura Aliyu, tsohon mataimaki na musamman na gwamnan jihar Katsina kan shirin ci gaban al’umma (CDP), bisa zargin shirya sace wani yaro mai shekaru takwas.

A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar, an kama Aliyu, mai shekaru 39, tare da wasu mutane biyar da ake zargi da shirya sace yaron.

Kakakin ‘yan sandan ya bayyana cewa an sace yaron a ranar 13 ga Mayu, 2026, da misalin ƙarfe 6:00 na yamma yayin da yake dawowa daga makarantar Islamiyya.

Ya ce waɗanda ake zargin sun tuntuɓi iyayen yaron kwana ɗaya bayan sun yi garkuwa da shi inda suka nemi a biya su kuɗin fansa Naira miliyan 50, amma bayan tattaunawa, an biya su Naira miliyan 17 don a saki yaron.

Rundunar ta ƙara da cewa an samu Naira miliyan 7.5, wanda ya kasance wani ɓangare na kuɗin fansa, an kuma samu wata motar Peugeot 307, babur ƙirar Boxer da sauran kayayyaki daga waɗanda ake zargin yayin bincike.

A cewar ‘yan sanda, waɗanda ake zargin sun amsa laifin a lokacin da ake yi musu tambayoyi kuma sun cewa akwai wani Abdul, wanda a halin yanzu rundunar ke nemansa ruwa jallo, a matsayin wanda ya taimaka musu wajen sace yaron.

Sanarwar da rundunar ‘yan sandan ta fitar ta ce “Bayan samun bayanan sirri, jami’an rundunar sun bi diddigin kuma sun kama mutane shida da ake zargi da hannu.

“Waɗanda aka kama su ne: Nura Aliyu, mai shekaru 39, wanda aka gano a matsayin wanda ya shirya garkuwa da yaron, kuma maƙwabcin iyayen yaron; Abubakar Aminu, mai shekaru 37; Ibrahim Muhammad, mai shekaru 51; Iliyasu Sani, mai shekaru 51; Abubakar Muhammad, mai shekaru 27; da Abdullahi Isma’il, mai shekaru 30.”

Kakakin rundunar ya bayyana cewa ana ci gaba da ƙoƙarin kama wanda ya gudu don gurfanar da su a gaban kotu bayan an kammala bincike.

By ukarofi