Da Ɗumi-Ɗumi: Pantami ya samu titin tsaya wa takarar gwamna a Gombe bayan koma wa PDP

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya koma jam’iyyar PDP, sannan ya samu tikitin tsaya wa takarar gwamna a jam’iyyar.

Ya zama ɗan takarar ne bayan wata sanarwar baka daga Shugaban kwamitin zaɓen fidda, Gregory Yenlong yayin zaɓen fidda gwani da aka yi a yau a Talata a Gombe.

Da yake jawabi jim-kaɗan bayan nasarar, Pantami ya ce ya tsaya takarar kujerar ne domin hidimta wa al’ummar jihar a wajen yin shugabanci na gaskiya da adalci matuƙar aka zaɓe shi a 2027.

A yanzu dai Pantami zai kara ne da Jamilu Gwamna da jam’iyya mai mulki APC ta tsayar a ɗaya ɓangaren.

Da fari, Pantami ya yi watsi da sulhun da APC ta yi na tsayar da Gwamna a matsayin ɗan takarar gwamna a APC, lamarin da ya sanya Shehin malamin ficewa daga jam’iyyar.

A wata sanarwa bayan taron gaggawa da sauran ‘yan takarar gwamna a jam’iyyar suka fitar, su nce doka ba ɗan siyasa damar fita daga jam’iyya ba ya koma wata kuma ya samu tikitin takara bayan an gudanar da zaɓe.

Waɗanda suka yi ƙorafin sun haɗa da Alhaji Abdulkadir Hamma Saleh, ⁠Hon. Khamisu Ahmed Mailantarki, Hon. Usman Aliyu Garry da Misis ⁠Monica Kaltho.

By Babaji