Tsohon kocin Chelsea, Enzo Maresca ya zama sabon mai horar da ‘yan wasan Man City kan yarjejeniyar shekara uku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙwararren ɗan jaridar harkar wasanni, Fabrizio Romano ya tabbatar da cewa Enzo Maresca na ƙasar Italiya ya sanya hannu akan kwantaragin shekara uku na zama sabon kocin ƙungiyar Manchester City.

Wannan yarjejeniya ta nuna cewa kocin, mai shekaru 46 ya sake samun wata dama a ƙungiyar Turai zuwa watan Yunin 2029 tun bayan barin sa Chelsea a watannin baya.

Hakan na zuwa ne sakamakon barin Pep Guardiola ƙungiyar a ƙarshen kakar wasan bana, bayan shafe kusan shekaru goma yana horar da ‘yan City.

Maresca ya kasance mataimakin Guardiola ne a baya, inda suka yi nasarar lashe muhimman kofuna ciki har da Champions League da Premier League da dai sauran su.

Rahotanni su bayyana cewa, bayan kwamitin jagororin ƙungiyar, Guardiola na daga cikin waɗanda suka nuna amincewarsu da ƙwarewar Enzo Maresca wajen horar da ‘yan wasa.

By Babaji