
Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi watsi da sakamakon zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, yana mai cewa babu adalci da gaskiya a ciki.
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X bayan zaɓen da aka gudanar ranar Talata, Amaechi ya zargi masu shirya zaɓen da hana wasu masu kaɗa ƙuri’a damar yin zaɓe tare da aikata maguɗin zaɓe.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Rivers ya bayyana sakamakon da jam’iyyar ta sanar a matsayin wanda aka ƙirƙira, yana mai cewa ba zai amince da duk wani sakamako da ba a yi cikin gaskiya da adalci ba.
Amaechi ya ce an samu kura-kurai masu yawa da suka shafi tsarin zaɓen, lamarin da ya jefa ayar tambaya kan sahihancin sakamakon da aka fitar.
