
Hukumar Yaƙi da Rashawa EFCC, ta tura tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, zuwa gidan yarin Kuje bayan kotu ta same shi da laifin cin hanci da rashawa.
Mai shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ne ya bayar da umarnin a ranar Talata.
Tun a ranar 7 ga watan Mayu kotun ta same shi da laifi kan tuhume-tuhume goma sha biyu da EFCC ta shigar, inda ta yanke masa hukuncin daurin shekaru saba’in da biyar a gidan yari saboda rashin halartar zaman yanke hukunci.
Kotun ta kuma bayar da umarnin kamo shi bayan ya ɓace, kafin daga bisani EFCC ta sanar da cafke shi a jihar Kaduna a ranar 19 ga watan Mayu.
A zaman kotun na ranar Talata, wani da ya gabatar da kansa a matsayin ɗan uwansa ya ce Mamman ya tafi Kaduna ne domin neman maganin gargajiya saboda rashin lafiya.
Mai shari’a Omotosho ya bayyana cewa hukuncin zaman gidan yarin ya fara aiki daga ranar Talata.
Haka kuma EFCC ta roƙi kotun ta amince da ƙwace wasu kadarori biyar da ake zargin suna da alaƙa da tsohon ministan a Abuja da Kaduna.
Kotun ta ɗage sauraron ƙarar ƙwace kadarorin zuwa ranar takwas ga watan Yunin shekarar 2026.
