
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamna Dikko Umar Raɗɗa na Jihar Katsina ya dakatar da babban mai taimaka masa na musamman akan ci-gaban al’umma, Alhaji Nura Aliyu Garwa bisa zargin sa da hannu a garkuwa da wani ɗan shekara 8 mai suna Imam Abubakar.
Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na jihar, Dakta Bala Salisu Zango ne ya sanar da haka a ranar Litinin.
Ya ce, ana zargin Nura Aliyu Garwa ne da hannu a sace yaron a yankin rukunin gidajen Sardauna da ke cikin garin Katsina, lamarin da ya sanya gwamnan ya dakatar da shi daga muƙamin.
Ya ƙara da cewa, a baya gwamnatin ta dakatar da Garwa akan samun sa da hannu a karkatar da kayayyakin tallafin bunƙasa al’umma a Ƙaramar Hukumar Batsari ƙarƙashin shirin gwamnatin akan ci-gaban al’umma.
Gwamna Raɗɗa ya kuma koka da faruwar al’amarin musamman ganin yadda ya ƙunshi ɗaya daga cikin manyan mutane a jihar, wanda ya ma taɓa yin takarar neman kujera a Majalisar Wakilai.
Raɗɗa ya kuma jinjina wa rundunar ‘yan sanda bisa hoɓɓasa da ta yi tare da sauran hukumomin tsaro wajen ƙoƙarin tabbatar da tsaro a jihar, yana mai kira ga jama’a da su riƙa taimakawa ta samar da bayanan ababen zargi a yankunansu.
A baya ne ‘yan sanda suka gurfanar da wasu da ake zargi da yin awon-gaba da wani ɗan shekara 8 a Katsina, inda aka gano cewa Nura Aliyu shi ne jagoransu.
Blueprint.ng ta ruwaito cewa, maƙocin su Imam Abubakar, wato Nura Aliyu ne wanda ya sace shi a lokacin da yake koma wa gida daga Islamiyya a ranar 13 ga Mayu, 2026 da misalin ƙarfe 6 na yamma.
