
Ƙungiyar Kiristoci (CAN) ta ware 14 ga Yuni, 2026 a matsayin ranar “Black Sunday” domin tunawa da waɗanda ta’addanci ya rutsa da su a Nijeriya.
CAN ta sanar da ware ranar Lahadin a faɗin Nijeriya ne domin girmama tare da tunawa da mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren ta’addanci da sauran nau’o’in rikicin tashin hankali a ƙasa baki ɗaya.
A cikin sanarwar da ta fitar bayan taron manyan shugabannin cocin ƙasa na shekarar 2026, Shugaban CAN, ya bayyana cewa za a gudanar da shirin addu’o’i na kwanaki uku daga 12 zuwa 14 ga Yuni, domin neman taimakon Ubangiji kan taɓarɓarewar tsaro a ƙasar.
Ƙungiyar ta bayyana cewa addu’a kaɗai ba za ta wadatar ba wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro, inda ta buƙaci gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa.
Daga cikin buƙatun da ƙungiyar ta gabatar akwai ayyana dokar ta-ɓaci akan tsaro, kafa rundunar ‘yan sanda ta jihohk, da kuma rage tsakatsakin tsarin tsaro domin inganta saurin ɗaukar mataki idan barazana ta taso
Haka kuma, CAN ta yi kira da a sako mutanen da aka yi garkuwa da su, tare da tabbatar da an yi wa waɗanda abin ya shafa adalci.
Matakin nan na zuwa ne a yayin da Nijeriya ke cigaba da fuskantar matsalolin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar.
