
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Laraba Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa mutane huɗu na ƙungiyar ta’addanci ta Al-Shabaab hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa hannu a laifin farmakin Cocin St. Francis Catholic Church da kaa ƙaddamar a ranar 5 ga watan Yunin 2022, wanda ya yi ajalin mutane 40 da raunata sama da wasu guda 100.
Mai Shari’a Emeka Nwite ya gabatar da hukuncin akan Idris Abdulmalik Omeiza mai shekaru 25; Al Qasim Idris, mai 20; Jamiu Abdulmalik mai 26; da kuma Abdulhaleem Idris ɗan shekara 25, bisa laifuka tara masu alaƙa da ta’addanci da aka danganta musu da Hukumar ‘Yan sandan Farin Kaya ta shigar akansu a madadin Gwamnatin Tarayya.
Sannan, kotun ta sallami mutum na biyar da ake tuhuma mai suna Momoh Otuho Abubakar ɗan shekara 47 bayan ta gano cewa babu isassun hujjoji da suke tabbatar da hannunsa a laifin harin.
Alƙali Nwite ya bayyana cewa binciken da aka gudanar akansu ya nuna cewa an tabbatar da hannun mutane huɗun mambobi ne na ƙungiyar ta’addancin kuma suna da hannu a mummunan harin.
A cewar lauyan da ya gabatar da ƙarar, maharan sun kutsa ne cikin Cocin inda suka karkashe mutane da dama, raunata wasu da kuma kame wasu a matsayin fursunonin yaƙi.
Ya ƙara da cewa, maharan sun yi amfani ne da ababen fashewa da bindiga ƙirar AK-47 wajen ƙaddamar da harin don ƙarfafa ayyukansu na nuna tsatstsauran ra’ayin addini.
Wannan hukunci ya kawo ƙarshen ɗaya daga cikin manyan shari’o’in ta’addanci a Nijeriya tun daga mummunan harin na 2022 da ya jefa fargaba acikin al’ummar ƙasa da kuma janyo yin alla-wadai daga ciki da wajen Nijeriya.
