Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta ci gaba da tallafa wa iyalan waɗanda hare-haren ‘yan bindiga suka shafa, inda kwamitin rabon tallafin ya kai ziyara a garin Jiƙamshi domin rabon tallafin ga waɗanda suka rasa rayukansu da kuma waɗanda suka samu raunuka.
Mutane 19 ne suka amfana da tallafin da ya kai jimillar Naira miliyan 2.3. Daga cikin waɗanda suka amfana akwai iyalan mutum tara da aka kashe, inda kowanne su ya karbi Naira N200,000, yayin da mutane 10 da suka samu raunuka suka karbi Naira N50,000 kowannensu.
Kwamitin ya kuma miƙa saƙon ta’aziyya da jaje ga Gwamnan Jihar Katsina ga iyalan wadanda suka rasu tare da addu’ar Allah Ya jikansu, Ya kuma bai wa waɗanda suka jikkata lafiya.
Mambobin kwamitin da suka halarci rabon tallafin sun haɗa da babban mataimaki na musamman kan harkokin tallafi ga Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Muhammad Lawal Zubairu, mai bai wa Gwamna Shawara kan Fasaha, Alhaji Abubakar Hamisu, Abdullahi Sani Abukur da kuma Abdulsalam Danjuma.
Bayan kammala rabon tallafin a Jiƙamshi, kwamitin ya wuce hedikwatar rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina, inda suka kai tallafin Naira miliyan ɗaya ga iyalan marigayi Sufeto Yusuf Usman, wanda aka kashe yana bakin aikinsa.
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Katsina, CP Ali Umar Fagge, ya tarbi mambobin kwamitin , inda aka miƙa tallafin ga iyalan marigayin tare da isar da saƙon jaje da ta’aziyya daga Gwamnatin Jihar Katsina.
Da yake jawabi, CP Ali Umar Fagge ya nuna godiyarsa ga Gwamnatin Jihar Katsina bisa wannan karamci da kulawar da take bai wa iyalan jami’an tsaro da sauran waɗanda hare-haren miyagu suka shafa. Ya kuma yaba wa kwamitin bisa yadda suke gudanar da aikinsu cikin adalci da jajircewa.
Shugaban kwamitin kuma mataimaki na musamman Muhammad Lawal Zubairu ya jaddada ƙudirin gwamnatin Katsina na cigaba da tallafa wa waɗanda matsalolin tsaro suka shafa tare da rage musu raɗaɗin halin da suka tsinci kansu a ciki.
