Kotu ta ɗage sauraron ƙarar ƙalubalantar shugabancin David Mark a ADC zuwa 8 ga Yuni

Spread the love

Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta ɗage sauraron ƙarar da Nafiu Bala Gombe ya shigar akan shugabannin tsagi na jam’iyyar ADC ƙarƙashin jagorancin David Mark zuwa ranar 8 ga watan Yuni.

Mai Shari’a Peter Lifu ne ya yi hukuncin bayan lauyan mai ƙara ya nemi ƙarin lokaci sakamakon rashin halartar lauyoyin ɓangarorin da ke neman shiga cikin shari’ar.

A zaman kotun, wakilan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, Independent National Electoral Commission, da kuma masu neman shiga cikin ƙarar ba su halarta ba, duk da cewa an tabbatar da cewa an aika wa INEC takardar sanarwar zaman kotun.

Lauyoyin waɗanda ake ƙara, ciki har da David Mark da sauran shugabannin ADC, ba su yi adawa da buƙatar ɗage shari’ar ba, sai dai sun nuna damuwa kan jinkirin da ake samu a shari’ar duk da umarnin da Kotun Ƙoli ta bayar na gaggauta sauraronta.

Mai shari’a Peter Lifu ya bayyana cewa kotun za ta yi aiki da umarnin Kotun Ƙoli da Kotun Ɗaukaka Ƙara na gaggauta sauraron shari’ar, tare da ɗaukar alhakin rashin kai wa wasu ɓangarori takardun gayyata cikin lokaci.

Daga nan ne kotun ta umarci a kai wa duk masu neman shiga cikin ƙarar takardun kotu cikin sa’o’i 24, sannan ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 8 ga Yuni domin cigaba da zama akan al’amarin.

By Babaji

Leave a Reply