Matsalar marasa gidaje a Nijeriya na iya kai wa miliyan 28 – Masana

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Jihar Legas ta yi gargaɗin cewa matsalar aarancin gidaje a Nijeriya na ci gaba da ƙamari, inda ta bayyana cewa giɓin gidaje a ƙasar na iya kaiwa kusan gida miliyan 28 nan gaba idan ba a ci gaba da ɗaukar matakan gaggawa ba. Kwamishinan Gidaje na Jihar Legas, Moruf Akinderu-Fatai, ne ya bayyana hakan yayin da yake bayani kan halin da fannin gidaje ke ciki a Nijeriya.

Ya ce, bayanan da Kwamitin Fasaha Kan Bayanai Na Gidaje Na ƙasa, wanda Ma’aikatar Gidaje da Raya Birane ta Tarayya ta kafa, suka tattara sun nuna cewa giɓin gidaje na hukuma a Nijeriya ya kai gida miliyan 14.925.

Sai dai ya ce matsalar ta fi haka muni, domin an gano cewa akwai karin gidaje miliyan 15.2 a faɗin ƙasar da suka lalace ko kuma ba su cika ƙa’idojin zaman lafiya da inganci ba. A cewarsa, idan aka haɗa waɗannan alƙaluma, jimillar ƙarancin gidaje da Nijeriya ke fuskanta na kusantar gida miliyan 28.

Akinderu-Fatai ya bayyana cewa wannan giɓin na haifar da barazana ga ci gaban birane, tattalin arziki da zaman lafiyar al’umma, musamman a manyan biranen da ke saurin faɗaɗa kamar Legas.

Ya ce, Legas, wadda ake hasashen tana da al’umma sama da miliyan 17.8, tare da yawan karuwar jama’a da ke kaiwa kusan kashi 3.8 cikin ɗari a duk shekara, ita ce cibiyar da ake fi buƙatar gidaje a Nijeriya. A cewarsa, yawaitar ƙaura daga karkara zuwa birane, ƙarancin filaye da kuma saurin bunƙasar birane na ci gaba da ƙara tsananta matsalar gidaje a jihar.

Rahotanni masu zaman kansu sun nuna cewa gibin gidaje a Legas kaɗai ya haura gida miliyan 3.3.

Kwamishinan ya ce matsalar ta fi tsanani ne a ɓangaren gidajen masu ƙaramin da matsakaicin ƙarfi, inda tsadar gidaje ke hana mutane da dama mallakar muhalli.

Duk da haka, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Legas sun ƙara ƙaimi wajen magance matsalar ta hanyar sauye-sauyen manufofi, shirye-shiryen samar da gidaje da kuma haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu. Ya ambaci wasu shirye-shiryen gwamnatin tarayya da suka haɗa da Asusun Zuba Jari Na Gidaje Na Kamfanin Ma’aikatar Kuɗi (MREIF), wanda ke samar da lamunin gidaje da riba mai sauƙi ta kashi 9.75 cikin ɗari, tare da damar biyan kuɗin cikin shekaru 20.

Akinderu-Fatai ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Jihar Legas ta samar da gidaje 10,623 cikin shekaru bakwai da suka gabata ta hanyar kuɗaɗen gwamnati da kuma haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu. Ya ce ana sa ran yawan gidajen zai haura 14,000 kafin ƙarshen shekarar 2026 sakamakon ayyukan da ake ci gaba da aiwatarwa.

A cewarsa, gwamnatin jihar na ci gaba da ƙoƙarin rage matsalolin mallakar gida tare da ƙara yawan gidaje masu sauƙin araha ga mazauna Legas. Ya ƙara da cewa shirye-shiryen samar da gidajen ba wai kawai suna magance matsalar muhalli ba ne, har ma suna samar da ayyukan yi tare da ƙarfafa harkokin gine-gine da kasuwancin kadarori a jihar.

By ukarofi

Leave a Reply