Konate ya yi bankwana da Liverpool bayan shekara biyar a Anfield

Spread the love

Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ta tabbatar da cewa ɗan wasan baya na ƙasar Faransa, Ibrahima Konate, zai raba gari da ƙungiyar a ƙarshen wannan kakar wasa bayan tattaunawar sabunta kwantiraginsa ta ci tura.

Konate mai shekaru 26 a duniya, wanda ya koma Liverpool daga ƙungiyar RB Leipzig ta Jamus a shekarar 2021, bai cimma matsaya da mahukuntan ƙungiyar ba kan sabon kwantiragi. Hakan na nufin zai bar filin Anfield kyauta da zarar yarjejeniyarsa ta kare a ƙarshen watan Yuni, bayan ya shafe shekaru biyar yana taka leda a Merseyside.

A cikin wata sanarwa da Liverpool ta wallafa a shafinta na hukuma, ƙungiyar ta ce Konate zai bar ƙungiyar bayan karewar kwantiraginsa a wannan bazarar, lamarin da zai kawo ƙarshen zamansa na shekaru biyar tare da “The Reds”.

Tun bayan zuwansa Liverpool, Konate ya buga wasanni 183 a dukkan gasa, inda ya zura ƙwallaye bakwai. A lokacin zamansa ya taimaka wa ƙungiyar lashe manyan kofuna da suka haɗa da gasar Firimiya ta Ingila ta kakar 2024/2025, Kofin FA, Kofin Carabao sau biyu da kuma Community Shield.

A saƙon ban kwana da ya aika wa magoya bayan Liverpool, Konate ya bayyana cewa yana cike da alhini saboda rashin samun damar yin ban kwana da magoya baya yadda ya kamata a filin Anfield.

Ya ce, ya isa Liverpool shekaru biyar da suka gabata a matsayin matashin ɗan wasa mai cike da manyan buri, amma yanzu yana barin ƙungiyar da tarin abubuwan tunawa da ba zai taɓa mantawa da su ba.

Konate ya ce sanya rigar Liverpool wata babbar ni’ima ce a gare shi, yana mai tuna lokutan farin ciki, ƙalubale, nasarori, abokantaka da kuma wasu lokutan baƙin ciki da suka haɗa da rasuwar abokin wasansu Diogo.

ɗan wasan na Faransa ya kuma bayyana irin mawuyacin halin da ya shiga bayan rasuwar mahaifinsa a bana, yana mai cewa duk da wannan jarrabawa, bai taɓa sassauta jajircewarsa ga Liverpool ba.

Ya gode wa abokan wasansa, masu horaswa, jami’an ƙungiyar da kuma magoya bayan Liverpool bisa irin goyon bayan da suka ba shi tsawon shekarun da ya yi a ƙungiyar.

Konate ya bayyana Anfield a matsayin wani wuri na musamman da ke cike da sihiri, yana mai cewa zai ci gaba da ɗauke Liverpool a zuciyarsa duk inda ya je.

A ƙarshe, ya bayyana cewa lokaci ya yi da zai fara sabon babi a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa tare da neman sabon ƙalubale, yana mai fatan sake haɗuwa da magoya bayan Liverpool a nan gaba.

By ukarofi