Kotu ta haramta biliyan N110 na alawus da siyan motocin ‘yan Majalisar Dokokin Ƙasa

Spread the love

Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, ta ayyana kashe Naira biliyan 110 da Majalisar Dokokin Ƙasa ta yi wajen sayen motoci da kuma biyan alawus ga sabbin ‘yan majalisa a matsayin abin da ya saɓa wa doka.

A hukuncin da Mai Shari’a Yellim Bogoro ta yanke, kotun ta ce kashe Naira biliyan 40 wajen sayen motoci 465 ga ‘yan majalisa da kuma Naira biliyan 70 a matsayin tallafin alawus ga sabbin mambobin majalisar ya karya dokokin saye da sayarwa na gwamnati, kundin tsarin mulki da kuma amanar da jama’a suka ɗora wa masu mulki.

Shari’ar dai ƙungiyar kare haƙƙin tattalin arziki da tabbatar da gaskiya da riƙon amana ta SERAP ce ta shigar tun a shekarar 2023, bayan bayyana shirin kashe waɗannan kuɗaɗe a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da matsin tattalin arziki.

Mai Shari’a Bogoro ta ce girman kuɗaɗen da aka ware tare da rashin gamsassun hujjojin bin ƙa’idojin sayen kaya na gwamnati ya sa kotun ta yanke cewa matakin ya kasance na son rai kuma bai dace da ƙa’idojin doka ba.

Kotun ta kuma bayyana cewa kasancewar waɗanda suka amince da kashe kuɗin su ne za su amfana da su kai tsaye, hakan na nuna yi wa kai gata da kuma rikicin anfani.

A cewar kotun, ‘yan majalisa ba za su iya fakewa da tsarin raba madafun iko ba domin kauce wa binciken halaccin yadda ake kashe kuɗaɗen jama’a, tana mai jaddada cewa kotuna na da ikon sa baki idan an samu zargin karya kundin tsarin mulki ko dokokin ƙasa.

Haka kuma kotun ta umarci Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da su tabbatar cewa duk wata kashe kuɗin gwamnati ko sayayya da Majalisar Tarayya za ta yi nan gaba ta bi cikakken tsarin doka tare da tabbatar da gaskiya, riƙon amana da kuma amfani da kuɗin jama’a yadda ya kamata.

SERAP ta bayyana hukuncin a matsayin babban nasara ga yaƙi da cin hanci da tabbatar da gaskiya a harkokin gwamnati, yayin da fitaccen lauya Femi Falana ya yaba da hukuncin, yana mai cewa rayuwar jin daɗin da wasu masu mulki ke yi a lokacin da jama’a ke cikin ƙunci ba za ta samu hujjar karewa ba.

By ukarofi

Leave a Reply