
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Litinin Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Mista Joseph Olasunkanmi Tegbe a matsayin sabon Ministan Wutar Lantarki da kuma Ambasada Sola Enikanolaiye a matsayin Ƙaramin Ministan Harkokin Waje.
A cewar wata sanarwa daga Kakakin Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, an gudanar da taron rantsarwar ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a gaban iyalan sababbin ministocin da kuma wasu manyan jami’an gwamnati.
Bayan murabus ɗin Yusuf Tuggar da Adebayo Adelabu a muƙaman ministocin harkokin waje da lantarki domin harkar siyasarsu, Shugaba Tinubu ya zaɓi sababbin ministocin biyu domin maye guraben bayan Majalisar Dattawa ta tantance su a ranar 6 ga watan Mayu, 2026.
An haifi sabon ministan lantarkin, Joseph O. Tegbe ne a Ibadan, Jihar Oyo, wanda ƙwararre ne a harkar tattali da sanin dabarun sauye-sauyen cibiya da ya shafe tsawon sama da shekaru 35 a fagagen gwamnati da na ‘yan kasuwa yana aiki.
Haka ma, Sola Enikanolaiye, wanda ɗan garin Igbagun ne na Jihar Kogi ne, wanda ya yi aiki a ma’aikatar harkokin waje tun daga shekarar 1982 har ya kai matakin darakta. Ya kuma yi aiki a matsayin jakadan Nijeriya a ƙasashen Habasha, Sabiya, Kanada da kuma Birtaniya a Landon.
