UTME ta 2026: JAMB ta buƙaci waɗanda aka shirya wa sabuwar jarrabawa su fitar da takardun shaida

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB), ta yi kira ga ɗaliban da aka sake shirya wa jarrabawar UTME ta 2026 da su fitar da takardar shaidarsu gabanin ranar rubuta ta, wato 13 ga Yuni.

A wata sanarwa da JAMB ta fitar a ranar Litinin ta bakin Kakakinta, Fabian Benjamin, ta ce a yanzu waɗanda suka cancanta suna da damar fitar da takardar bayan ta buɗe sahihin shafinta.

Benjamin ya ce, takardar ta ƙunshi bayanai kamar cibiyar da ɗalibi zai rubuta, rana, lokaci da wasu dokoki da suka shafi jarrabawar.

Ya kuma ce, an ɗauki matakin ne domin ba wa waɗanda suka samu tsaiko a jarrabawar farko na na’ura musamman akan lamuran tantancewa.

Akan haka ne ya shawarci ɗaliban da lamarin ya shafa da su hanzarta ziyartar sahihin shafin JAMB na yanar gizo don samun takardar bayanan jarrabawar tasu domin kauce wa sake shiga matsala.

By Babaji

Leave a Reply