Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babbar Kotun Jihar Filato mai lamba ta 17 ta yanke hukuncin cewa, duk wani Bahaushe da aka haifa kuma ya taso a ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa yana da cikakken haƙƙin a ɗauke shi a matsayin ɗan asalin yankin.
Alƙali C. Donglong ne ya yanke hukuncin yayin da yake yanke hukunci a ƙarar da Fatima Baba Akawu da Baba Alhaji Akawu suka shigar a gaban kotun kan ƙin ba Fatima takardar shaidar asali (Certificate of Indigene) daga ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.
Masu ƙarar sun nemi kotun ta tantance ko Fatima Baba Akawu, wadda aka haifa a Jos ta Arewa kuma mahaifinta cikakken ɗan asalin yankin ne, tana da haƙƙin a amince da ita a matsayin ’yar asalin yankin duk da kasancewarta ’yar ƙabilar Hausa.
Sun kuma nemi kotun ta yi hukunci kan ko ƙin ba ta takardar shaidar asali tare da ba ta takardar zama (Residential Certificate), alhali an ba wani mai suna Dung Bot daga kabilar Berom takardar shaidar asali a ranar guda, ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Nijeriya da kuma dokokin kare haƙƙin ɗan Adam.
Har ila yau, masu ƙarar sun yi tambaya kan ko matsayin Baba Alhaji Akawu a matsayin cikakken zan asalin Jos ta Arewa kuma tsohon ɗan majalisar wakilai mai wakiltar yankin a shekarar 1983 ya bai wa ’ya’yansa damar samun takardar shaidar asalin yankin.
Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Donglong ya amince da dukkan buƙatun masu ƙarar, yana mai cewa bayan nazarin dukkan hujjoji da takardun da aka gabatar, kotun ta gamsu cewa ƙarar tana da tushe kuma ta cancanci samun nasara.
Ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanadi kariya ga kowane ɗan ƙasa daga nuna wariya bisa ƙabila ko yanayin haihuwa.
Mai shari’ar ya soki matakin da ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa ta ɗauka na bai wa Fatima takardar zama saboda kasancewarta Bahaushiya, yayin da aka bai wa Dung Bot daga ƙabilar Berom takardar shaidar asali.
A cewarsa, wannan mataki wariya ce ta ƙabila wadda ta saɓa wa ruhin da kuma tanadin kundin tsarin mulkin Nijeriya.
