Borno: Mayaƙan Boko Haram sun cinna wa makarantu wuta a Chibok

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram/ISWAP ne, sun cinna wuta a makarantar firamare da wata sakandare a ƙauyen Kautikari da ke Ƙaramar Hukumar Chibok a Jihar Borno, lamarin da ya ƙarfafa damuwa akan rashin tsaron makarantu da ƙauyukan a shiyyar mai fama da matsalolin tayar da ƙayar baya.

Rahotanni sun bayyana cewa, harin na zuwa ne makonni da sace ɗaliban Makarantar Firamare da Ƙaramar Sakandare a Askira-Uba da aka riƙe su har na tsawon kusan wata guda babu labarinsu, wanda ke nuna cigaba da razanarwar da ƙungiyoyin tayar da ƙayar baya ke yi a sassan jihar Borno.

A cewar majiyoyin tsaro, maharan sun kutsa cikin Kautikari ne da misalin ƙarfe 7 na yammacin ranar Asabar, inda suka jefa tsoro acikin jama’ar yankin tare da tilasta wa wasu tserewa yayin da ‘yan ta’adda suke harin cibiyoyin ilimi a ƙauyen.

Ɗaya daga cikin majiyar ta ce, duk da cewa babu batun jikkata ko mutuwa yayin haɗa rahoton, farmakin ya haddasa firgici acikin ƙauyen.

Mazauna yankin sun ce ‘yan ta’addar sun banka wa makarantun firamaren da na sakandaren a ƙauyen wuta, wanda ya yi sanadiyyar lalata cibiyoyin ilimin yara a ƙauyen.

Wani mazaunin Kautikari ya ce, duka da cewa sun riƙa fuskantar hare-haren mayaƙan ‘yan ta’adda, ba a taɓa samun lokacin da aka lalata cibiyoyin ilimi ba sai a wannan hari.

Ya bayyana cewa, wata guda da ya gabata ‘yan ta’adda sun farmaki Kautikari ba tare da lalata kowane waje ba, inda ake ganin na yanzun a matsayin mai tayar da hankali.

Yunƙurin ji ta bakin Kakakin Rundunar ‘Yan sandan Borno, ASP Nahum Kenneth Daso bai yi nasara ba sakamakon rashin amsa kira da saƙonnin da aka tura masa don ji ta bakinsa.

By Babaji

Leave a Reply