Kotu ta umarci INEC ta soke rajistar jam’iyyar ADC da wasu huɗu

Spread the love

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ta soke rajistar jam’iyyun siyasa guda biyar, ciki har da African Democratic Congress (ADC), bisa zargin gaza cika sharuɗɗan da kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada domin ci gaba da kasancewa a matsayin halastattun jam’iyyun siyasa.

Sauran jam’iyyun da hukuncin ya shafa sun haɗa da Action Peoples Party (APP), Action Alliance (AA), Accord Party (AP) da Zenith Labour Party (ZLP). Mai shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin bayan sauraron ƙarar da ƙungiyar tsofaffin ‘yan majalisa ta ƙasa ta shigar a gaban kotun.

Masu ƙarar sun bayyana cewa jam’iyyun sun gaza samun sakamakon da kundin tsarin mulki ya tanada, wanda ya haɗa da samun aƙalla kashi 25 cikin 100 na ƙuri’u a wata jiha yayin zaben shugaban ƙasa ko kuma lashe kujerar zaɓe a matakin tarayya, jiha ko ƙaramar hukuma. Sun ce jam’iyyun sun kasa yin hakan a zaɓukan shekarar 2023 da kuma zaɓukan cike gurbi da aka gudanar daga baya.

Ƙungiyar ta buƙaci kotu ta tilasta wa INEC soke rajistar jam’iyyun tare da hana su shiga harkokin siyasa, gudanar da gangami, zaɓen fidda gwani da sauran ayyukan jam’iyya. Masana siyasa na ganin cewa hukuncin na iya yin tasiri ga shirye-shiryen wasu ‘yan siyasa da ke da niyyar tsayawa takara a zaɓen shekarar 2027 ƙarƙashin jam’iyyun da hukuncin ya shafa.

By ukarofi

Leave a Reply