
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Herve Renard ya sake dowa wa harkokin ƙwallon ƙafa na Afirka bayan da ƙasar Tunisiya ta naɗa shi a matsayin mai horar da ‘ya wasanta.
Hukumar kuka da Harkokin Ƙwallon Ƙafa ta ƙasar (FTF) ta naɗa ɗan Faransan mai shekaru 57 ne a daren ranar Litinin wayewar Talata bayan sallamar Sabri Lamouchi.
Hakan na zuwa ne bayan da ‘yan Tunisiya suka sha kaye a wasansu da Sweden da aka tashi 5 da 1 a karawar farko a rukunin F na gasar Kofin Duniya na 2026.
Wannan mataki ya nuna an samu ƙasa ta farko a tarihin gasar da ta sallami koci daga kammala wasan farko.
FTF ta zaɓi Renard ne bisa ƙwarewarsa musamman ganin yadda ya jagoranci ƙasashen Zambiya da Ivory Coast lashe gasar Kofin ƙasashen Afirka a 2012 da 2015.
Wannan shi ne gasar Kofin Duniya na uku da Renard yake jagorantar wata ƙasa aciki bayan zama kocin Moroko da Saudiyya a 2018 da 2022, inda a na biyun ya yi nasara akan Argentina da ci 2 da 1 duk da cewa ita ta lashe kofin daga bisani.
