
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta kammala ɗaukar ɗan ƙasar Faransar nan, Ibrahim Konate daga kulob ɗin Liverpool a hukumance.
Ɗan wasan bayan ya rattaɓa hannun ne wa Madrid akan yarjejeniyar shekara huɗu sakamakon ƙarewa da kwantaraginsa ya yi a Merseyside.
A ranar Alhamis Real Madrid ta Laliga ta sanar da cewa, ɗan wasan mai shekaru 27 ya zama mallakinta har zuwa bazarar shekarar 2030, inda ake fatan kammala sauya sheƙar ɗan wasan bayan kammala gasar Kofin Duniya.
Konate ya koma Liverpool ne daga ƙungiyar RB Leipzig a shekarar 2021. Ya kuma bar “the Reds” ne bayan buga mata jimillar wasanni 183.
A yayin zamansa a Ingila, ya lashe kofin Premier League a 2025 da na FA a 2022.
A yanzu dai ɗan Faransar shi ne ɗan wasa na uku da Real ta siya a kakar cinikayyar ‘yan wasa a bana, bayan ta siyo Marc Cucurella da Bernardo Silve na Chelsea da Man City daga zuwan Jose Mourinho a matsayin sabon kocinta.
Kasancewar Madrid ta rasa damar lashe Laliga sau biyu a jere, a yanzu tana cigaba da ƙoƙarin ganin ta ɗauko Denzel Dumfries daga Inter Milan domin ƙarfafa harkokinta gabanin kakar wasa mai zuwa.
A wani ɓangare kuwa, Madrid ta tsawaita zaman ɗan wasa Antonio Rudiga har zuwa 2027, yayin da Dani Carvajal da David Alaba suka bar ƙungiyar bayan kwantaraginsu sun ƙare ba tare da sabuntawa ba.
