Yadda Atiku ya sa aka sari mahaifiyata a hannun ’yan ta’adda – Rarara

Spread the love

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Fitaccen mawaƙin siyasa a arewacin Nijeriya, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara, ya bayyana cewa, tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya janyo wasu ’yan ta’adda daban suka sari mahaifiyarsa, Hajiya Hauwau Adamu, a hannun ainihin waɗanda suka fara kama ta, kamar yadda ake sarar kaya a wajen cin kasuwa.

Rarara ya yi bayanin hakan ne a cikin makon nan yayin da yake mayar wa fitaccen mawaƙin kudancin Nijeriya Daɓid Adeleke, wanda aka fi sani da Daɓido. Idan za a iya tunawa, a makon jiya Daɓido ya fito idon duniya a yayin bukukuwan buɗe bikin gasar ƙwallon ƙafa ta Kofin Duniya ya sanya riga mai ɗauke da sunayen yara guda 39 da malamai bakwai da aka yi garkuwa da su a wata makaranta a jihar Oyo kwanakin baya yana mai kira da a tserar da su.

A cewar mawaƙi Rarara, yayata garkuwa da mutane da ake yi a kafafen sada zumunta ne yake ƙarfafa ta’addanci, domin yana janyo hankalin wasu ’yan ta’addar su je su yi cinikin waɗanda aka kama su amshe su, don su ƙara kuɗin fansa akan su.

A ta bakin Rarara ya ce, “lokacin da aka kama mahaifiyata abin da ya faru kenan. Waɗanda suka kama ta saura kaɗan…bai fi sauran awanni ba a cikin kwana bakwai – kwana takwas – a kama su, Atiku Abubakar ya je ya yi magana a ‘media’ ya ce ya kamata ’yan ta’adda su saki mamar Rarara.

“Daga wannan maganar da ya yi, wasu manyan ’yan ta’addar suka zo suka sare ta a hannun waɗannan yaran. Sai da muka ƙara wajen kwana 11  sannan muka samo Mama.

“Ka ga wannan cutar da ni ya yi. Wasu suna ganin kamar ya birge ni ne ko shi ya yi don ‘popularity’ ne… ya yi kaza, saboda mutane ‘followers’ ɗin shi yawanci sun yaɗa abin, to wannan maganar ta sa aka zo ya ƙara ƙa abin nisa.

“Wasu suna ganin Atiku ya yi alhini akaina, to ni cuta ta ya yi, don idan da gaske so yake yi ya taimaki mamana, kamata ya yi ya rubuta wa Shugaban ƙasa ‘letter’ ko kuma ya rubuta wa shuwagabannin tsaro; DSS da shi kuma IG, ya ce ya kamata wannan abin a yi duk yadda za a yi – idan ma shawara ce ya bayar tunda tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa ne, amma sai ya je ya yi magana ‘media’. Daga wannan maganar tashi sai da muka kwana 11 sannan aka sake ganin. Inda take. To, wannan cuta ce ko taimako ne? Ya kamata mu gane.”

Don haka Mawaƙi Rarara, wanda ya hyi fice wajen kare gwamnatin jam’iyyar APC a Nijeriya a ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga masu amfanin da kafafen sada zumunta da su guji yaɗa bidiyon ’yan ta’adda, domin hakan yana taimaka musu ne a cewarsa.

Kawo haɗa wannan rahoto dai, shi tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa kuma jagoran ’yan adawa a Nijeriya Atiku Abubakar bai mayar da martani ba.

By ukarofi

Leave a Reply