Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta bayyana cewa ta samu gagarumar nasara wajen kama mutane da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, tare da daƙile hare-haren masu garkuwa da mutane, ’yan fashi da makami da kuma masu alaka da ƙungiyoyin ta’addanci a sassa daban-daban na jihar.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kebbi, Umar M. Hadejia, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatar rundunar da ke Birnin Kebbi a ranar Laraba.
Ya ce nasarorin da aka samu sun biyo bayan sahihan bayanan sirri, bincike da kuma haɗin kan al’umma da jami’an tsaro ke samu wajen yaƙi da miyagun laifuka.
A cewarsa, rundunar ta kama wasu mutane da ake zargin suna da alaka da sabuwar kungiyar ta’addanci da ake kira Mamudawa da kuma wasu da ake zargin suna da alaƙa da Boko Haram a yankin ƙaramar Hukumar Bagudo.
Haka kuma, rundunar ta cafke wasu da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne a kan hanyar Bakin Ruwa zuwa Bagudo. Daga cikin waɗanda aka kama akwai Haruna Abubakar, Abubakar Lawali, Anme Shehu da kuma Yahaya Shehu, waɗanda ake zargin suna da mafaka a dajin Soda.
Rundunar ta kuma kama Murtala Sani daga ƙauyen Zazzagwa da ke Karamar Hukumar Argungu bayan samun bayanan sirri da suka nuna yana taimaka wa mayaƙan Lakurawa wajen gudanar da ayyukansu. Bincike ya nuna cewa yana samar musu da abinci da sauran kayan masarufi a maɓoyarsu.
A wani samame da rundunar ta kai, an samu nasarar ceto Malama Asma’u Isah, matar Mustapha Musa, mazauniyar unguwar Bayan Forestry a Birnin Kebbi, bayan da wasu ’yan fashi suka kai hari gidansu suka kwashe kayayyaki da kudade masu yawa. Rundunar ta kama daya daga cikin wadanda ake zargi da aikata laifin, mai suna Abubakar Siddi.
Haka zalika, jami’an tsaro sun kama Ayuba Ibrahim, mazaunin Bakin Ruwa, wanda ake zargin yana bai wa ’yan ta’adda bayanai. Binciken da aka gudanar a gidansa ya kai ga gano wasu kayayyaki da suka hada da bindiga da sauran abubuwan da ake zargin suna da alaƙa da ayyukan ta’addanci.
A wani ci gaba kuma, rundunar ta cafke Ahmed Sa’adu, wanda aka fi sani da “Baga”, bisa zargin satar wata mota ƙirar Mercedes da aka sace daga Jihar Sokoto. Kwamishinan ya ce ana ci gaba da farautar wani abokin aikinsa mai suna Kasimu Bunza, wanda ya tsere.
A ɓangaren laifukan cin zarafin yara kuwa, rundunar ta kama Faruku Muhammed, mai gadin wata makarantar Islamiyya da ke unguwar Tungar Zabarmawa a garin Jega, bisa zargin lalata wata yarinya mai shekaru 10 mai suna Naja’atu Surajo.
Bisa bayanan da rundunar ta fitar, wanda ake zargin ya yaudari yarinyar bayan an tashi daga makaranta, ya kai ta dakin gadi inda ya aikata abin da ake zargin ya saba wa doka.
Kwamishinan ’yan sandan ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike a kan dukkanin wadanda ake zargi, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike domin su fuskanci hukuncin da doka ta tanada.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai game da duk wani mutum ko gungun mutane da suke zargin suna da hannu a ayyukan laifi.
“Tsaro alhakin kowa ne. Hadin kan jama’a da jami’an tsaro zai taimaka matuka wajen tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma,” in ji Kwamishinan.
