2027: Idan na zama Shugaban ƙasa zan tattauna da ’yan bindiga – Peter Obi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Dan takarar Shugaban ƙasa na Jam’iyyar Nijeriya Democratic Congress (NDC), Mista Peter Obi, ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi a zaɓen 2027, gwamnatinsa za ta rungumi tattaunawa da ’yan bindiga da sauran masu aikata ta’addanci da suka nuna aniyar ajiye makamansu da rungumar zaman lafiya, yayin da za a yi amfani da ƙarfin gwamnati wajen murƙushe waɗanda suka ƙi daina tashin hankali.

Obi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a shirin BlackBoɗ with Rufai Oseni, inda ya yi bayanin yadda yake shirin magance matsalar tsaro da kuma ƙarfafa haɗin kan ƙasa idan ya samu damar jagorantar Nijeriya.

Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce samar da zaman lafiya mai ɗorewa na buƙatar bai wa masu son gyara halayensu dama su sake shiga cikin al’umma tare da ba da gudunmawa ga ci gaban ƙasa.

“Domin haɗa kan ƙasa, duk wanda yake son zaman lafiya zan yi magana da shi, zan tattauna da shi. Amma duk wanda yake son yaƙi, za mu yi yaƙi da shi,” inji Obi.

Ya ce Nijeriya ta kai wani mataki da ya kamata a ba wa waɗanda suka tuba damar sake farawa, maimakon a ci gaba da kallonsu da laifukan da suka aikata a baya.

A cewarsa, ci gaban al’umma yana samuwa ne idan aka samar da damar gyara rayuwa ga mutanen da suka nuna nadama tare da sauya halayensu.

Domin ƙarfafa hujjarsa, Obi ya kawo misalin wata jami’a da ya ziyarta a Amurka, inda ya ce wasu daga cikin shugabannin jami’ar sun taɓa zaman gidan yari kafin daga bisani su gyara rayuwarsu kuma su zama manyan malamai da shugabanni.

“Na taɓa ziyartar wata jami’a a Amurka inda daga shugaban sashen ilimi zuwa wasu manyan jami’ai, da dama daga cikinsu sun taɓa zaman gidan yari saboda wasu laifuka. Amma daga baya sun gyara rayuwarsu kuma suka zama masu amfani ga al’umma,” inji shi.

Obi ya kuma danganta matsalar tsaro da batun haɗin kan ƙasa, yana mai cewa dole ne kowace ƙabila, yanki da al’umma su ji suna da wakilci a cikin gwamnati da kuma rabon damar ci gaba.

Ya ce manufarsa ita ce gina Nijeriya mai cike da adalci, haɗin kai da damar daidaito ga kowa.

“Zan haɗa kan Nijeriya kuma in tabbatar babu wanda aka bari a baya. Babu wata ƙabila ko yanki da za a ware. Za mu nuna ƙauna, kulawa da adalci ga kowa,” inji ɗan takarar.

Kalaman Obi sun ƙara rura wutar muhawara kan hanyar da ta fi dacewa wajen magance matsalar rashin tsaro a Nijeriya, musamman batun ko ya kamata gwamnati ta ci gaba da amfani da ƙarfin soja kaɗai ko kuma ta haɗa shi da tattaunawa da masu ɗauke da makamai.

Yayin da wasu masana ke ganin tattaunawa na iya zama wani ɓangare na samar da zaman lafiya, wasu na ganin hakan na iya ƙarfafa masu aikata laifuka tare da rage tasirin matakan tsaro da ake ɗauka.

A kwanakin baya, wasu ’yan siyasa da masana shari’a, ciki har da fitaccen lauya Femi Falana (SAN), sun bayyana damuwa kan yiwuwar tattaunawa da ƙungiyoyin da gwamnati ke kallon a matsayin masu aikata ta’addanci.

Ana sa ran furucin na Peter Obi zai ci gaba da jawo muhawara a fagen siyasa da tsaro yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

By ukarofi