Kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙarar NBC, ta tabbatar da hana hukumar cin tarar gidajen rediyo da talabijin

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yi watsi da wani yunƙuri da Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta ƙasa (NBC) ta yi na soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya hana ta ci gaba da ƙaƙaba tara ga gidajen rediyo da talabijin.

A hukuncin da alƙalan kotun suka yanke baki ɗaya a ranar Laraba, kotun ta bayyana ƙarar ɗaukaka ƙarar da NBC ta shigar a matsayin wadda ke da manyan kurakurai na doka, saboda haka ba za ta iya ci gaba da sauraron karar ba.

Mai shari’a Jane Inyang, wadda ta karanta hukuncin kotun, ta bayyana cewa an samu babban kuskure a sunan ɓangaren da ya shigar da karar. Ta ce yayin da karar da aka yi a Babbar Kotun Tarayya ta kasance tsakanin Incorporated Trustees of Media Rights Agenda da National Broadcasting Commission (NBC), a takardar daukaka karar an rubuta sunan mai karar a matsayin Nigerian Broadcasting Commission, wanda ba shi ne sunan da aka yi amfani da shi a ƙarar asali ba.

A cewarta, wannan kuskure babban matsala ce ta doka da ta hana kotun samun ikon sauraron karar.

“Takardar ɗaukaka ƙarar da sauran bayanan da aka gabatar suna da manyan kurakurai na doka kuma ba za su iya bai wa wannan kotu hurumin sauraron karar ba,” in ji Mai Shari’a Inyang.

Kotun ta jaddada cewa sahihiyar takardar daukaka kara ita ce ginshikin kowace kara a matakin daukaka kara, kuma idan akwai matsala a kanta, to babu yadda kotun za ta ci gaba da sauraron karar.

Saboda haka, kotun ta yanke hukuncin cewa babu ingantacciyar kara a gabanta, ta kuma yi watsi da karar baki ɗaya.

ƙarar ta samo asali ne daga hukuncin da Mai Shari’a Rita Ofili-Ajumogobia ta yanke a ranar 17 ga Janairu, 2024, inda ta bayyana cewa NBC ta karya doka da kundin tsarin mulki lokacin da ta kakaba tarar Naira miliyan biyar-biyar ga kamfanonin MultiChoice Nigeria Limited (DStv), TelCom Satellite Limited (TStv), Trust TV Network Limited da NTA StarTimes Limited a watan Agustan 2022.

NBC ta ci tarar ne bayan wadannan kafafen yada labarai sun watsa wasu shirye-shiryen bincike da suka mayar da hankali kan matsalar ’yan bindiga da rashin tsaro a Jihar Zamfara, wanda hukumar ta ce ya saba wa muradun tsaron kasa.

Sai dai Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukuncin cewa matakin ya saba wa sashe na 39 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya da kuma sashe na 9 na Yarjejeniyar Kare Hakkin Dan Adam ta Afirka, wadanda suka tabbatar da ’yancin fadin albarkacin baki da kuma ’yancin jama’a na samun bayanai ba tare da tsangwama ba.

Wannan sabon hukunci na Kotun Daukaka Kara ya kara raunana kokarin NBC na kare ikonta na kakaba tara ga gidajen rediyo da talabijin.

A watan Afrilun 2026 ma, Kotun Daukaka Kara ta yi watsi da wata kara daban da NBC ta shigar domin kalubalantar hukuncin da Mai Shari’a James Omotosho ya yanke a ranar 10 ga Mayu, 2023.

A wancan hukuncin, kotun ta bayyana cewa tara hukunci ne na laifi wanda kotuna ne kadai ke da ikon kakaba shi, ba hukumomin gwamnati ko na gudanarwa ba.

Masana harkokin shari’a sun bayyana cewa wannan hukunci zai kara karfafa kariyar ’yancin kafafen yada labarai a Nijeriya, tare da takaita ikon NBC na kakaba tarar kudi ga gidajen rediyo da talabijin ba tare da samun umarnin kotu ba.

Ana ganin matakin zai kasance muhimmin ci gaba ga ’yancin aikin jarida da kare hakkin jama’a na samun sahihan bayanai kan muhimman batutuwan da suka shafi rayuwarsu da makomar kasa.

By ukarofi