
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta tsaurara matakan tsaro a Cibiyar Nazarin Manufofi da Dabarun Ƙasa (NIPSS) da ke Kuru a Jihar Filato.
Shugaba Tinubu ya bada umarnim ne sakamakon wani harin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa makarantar a kwanan nan.
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne ya bayyana haka yayin wakiltar Shugaban, inda ya kuma yi alƙawarin cewa Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa iyalan sojoji biyu da ɗan sanda guda da suka rasa rayukansu a harin.
Haka kuma, ya umarci mahukuntan NIPSS da su gabatar da cikakken rahoton tsaro cikin kwanaki uku domin inganta kariya da tsaron cibiyar.
A cewar Shettima, shugaban ƙasar ya bada umarnin gaggawan ne da domin aiwatar da a nan take ba tare da jinkiri ba, inda ake buƙatar Daraktan NIPSS ya yi aiki tare da jami’an tsaro don tabbatar da biyayya ga umarnin.
Kazalika, ya ce wajibi ne a fifita ba NIPSS kariya da tsaron da ya dace kasancewar tana ɗaya kadarorin ƙasa domin kauce wa sake faruwar harin ‘yan ta’adda a nan gaba.
