
Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Tunji Rilwan Disu, ya amince da naɗin CSP Anietie Okokon Edem Iniedu a matsayin sabon Kakakin rundunar, inda zai fara aiki nan take.
A sanarwar da rundunar ta fitar, an bayyana CSP Anietie Iniedu a matsayin ƙwararren jami’in ɗan sanda mai gogewa sosai a fannonin sadarwa da dabaru, tattara bayanan sirri, gudanar da ayyuka, da tabbatar da riƙon amana ga jama’a.
Kafin wannan naɗi, ya kasance shugaban Sashen Karɓar da Amsa Korafe-korafe (Complaint Response Unit) a Hedikwatar Rundunar da ke Abuja, inda ya jagoranci shirye-shiryen da suka ƙara inganta gaskiya da kuma ƙarfafa amincewar jama’a ga rundunar ‘yan sanda.
Jami’in, wanda ya fito daga Jihar Akwa Ibom, ya kuma taɓa zama Jami’in Hulɗa da Jama’a na Kwalejin Fasahar Sadarwa ta ‘Yan Sanda da ke Jihar Ogun.
Haka kuma ya riƙe muhimman muƙamai na gudanarwa da ayyuka, ciki har da matsayin Shugaban Dakin Bibiyar Lamurra (Situation Room) na Hedikwatar Rundunar.
Sufeto Janar na ‘Yan Sanda ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa CSP Iniedu zai taimaka wajen ƙarfafa dabarun sadarwa na rundunar, zurfafa hulɗa da jama’a, da kuma tallafa wa sauye-sauyen da ake aiwatarwa a harkar aikin ‘yan sanda ta hanyar ingantaccen gudanar da bayanai akan al’amuransu.
