
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Akwai saɓani game da zaɓukan fidda gwani da aka gudanar a sassa daban-daban na Nijeriya a jam’iyyar adawa ta NDC a ranar 29 ga watan Mayu.
Na kwanan nan shi ne wanda ya samu jam’iyyar a Jihar Ebonyi, musamman wajen yin murabus ɗin mambobin kwamitin zartarwarta.
A yayin haɗa wannan rahoto, sama da mambobi guda 11 ne na kwamitin zartarwarta na jihar suka fice daga NDC.
Daga saƙonnin da wakilin Blueprint.ng ya samu a ranar Litinin, waɗanda suka bar NDC a Ebonyi sun haɗa da Mataimakin Shugaban jam’iyyar; Kwamared Okey Idenyi, Sakatarenta; Barista Aduma Solomon Chinedu, Jagoran Matasa; Anthony Nwofe, Mataimakinsa; Emenike Daniel Oroke.
Sauran sune Jami’in Walwala; Hon. Ajah Cyril, da jagororin NDC na ƙananan hukumomi biyar da dai sauransu.
A cewar saƙonnin nasu, sun ɗauki matakin ne bisa la’akari da yadda aka gudanar da zaɓukan fidda gwanin na kwanan nan, waɗanda suka yi zargin cewa wani tsohon gwamnan jihar ya shirya maƙarƙashiya akansu.
Sun kuma zargin jagorancin jam’iyyar a mataki na ƙasa da fifita buƙatun tsohon gwamnan jihar Dakta Sam Egwu a madadin sauraren matsalolin al’umma da tushensu.
