
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Mashawartan Arewa (ACF) ta ƙaddamar da Kwamitin Samar da Kuɗaɗe da nufin tabbatar da tsare gaskiya da adalci wajen ciyar da harkokin ilimi da tattalin arziƙin al’umma gaba a sassan arewacin Nijeriya.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Talata, ta ce tsohon Sufeto Janar na Rundunar ‘Yan sanda, Muhammad Dikko Abubakar ne zai jagoranci kwamitin, inda aka ɗora masa nauyin sanya dabarun jagoranci da tabbatar da nasarar aiwatar da manufofin kuɗaɗen.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da kwamitin, Shugaban ACF kuma Wazirin Dutse, Alhaji Bashir Ɗalhatu ya bayyana godiyarsa ga mambobin ƙungiyar bisa sadaukarwa da goyon baya da kuma ƙoƙarinsu na tabbatar da aiwatar da manufofin ƙungiyar.
Ya bayyana cewa, shirin samar da kuɗaɗen zai wakilci gagarumin matakin ƙarfafa damarmakin ilimi, tallafa wa ci-gaban al’umma da samar da yanayin inganta ci-gaba a baki ɗaya shiyyar.
A cewarsa, ƙungiyar tana aiki tuƙuru da masu ruwa da tsaki, masu fafutukar samar da ci-gaba da jagororin al’umma domin gina zaman lafiya, haɗin kan al’umma, shugabanci na gari da ci-gaban ƙasa.
Ya bayyana cewa, ACF na fatan tara wa asusun kwamitin ne Naira biliyan 100, inda a nan take aka yi alƙawarin biliyan N7.8, amma zuwa yanzu Naira biliyan 3.9 ne a asusun ACF na Bankin Ja’iz.
Kazalika, ya tabbatar wa mambobin kwamitin cewa kuɗin na cikin aminci, yana mai kira ga waɗanda suka yi alƙawari da su cika domin tafiyar da al’amuran kwamitin yadda ya dace.
