Kofin Duniya: Ivory Coast ta haye zuwa rukunin ƙalubale bayan doke Curaçao

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon ɗan wasan Arsenal, Nicolas Pepe ya zura ƙwallo biyu a raga a wasan da Cote d’Ivoire ta yi da Curaçao a gasar Kofin Duniya na 2026, lamarin da ya ƙasar Afirkan damar hayewa zuwa rukunin ƙalubale.

Pepe na ɗaya daga cikin ‘yan wasan da aka sauya daga waɗanda suka sha kaye da ci 2 da 1 a hannun Jamus a wasa na biyu na matakin rukunin-rukuni.

A yanzu dai, Ivory Coast za ta haɗu da wanda ya ƙare a matsayi na uku daga rukunin I a birnin Dallas a ranar 30 ga Yuni.

By Babaji

Leave a Reply