Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
Duk dai ya ke a waɗansu sassan arewacin Nijeriya damina ta sauka, inda tuni manoma suka soma gyare-gyaren gonakinsu, don shirin noma, sai dai da yawa suna fargabar hare-haren ’yan bindiga, musamman a yankunan ƙananan hukumomin Augie, Arewa, Dandi, Bagudo, Suru, Koko, Shanga, Ngaski, Yauri, Danko/Wasagu da kuma Sakaba a Jihar Kebbi, waɗanda sune suka fi fuskantar ƙalubalen tsaro, saboda a kullum safiya sai an kai hari ko da rana ko kuma cikin dare.
Hare-haren da waɗannan ’ƴan bindiga ke kai wurare daban-daban yana ɗaukar salo daban-daban yayin da wani lokaci sukan kai mummunan hari su tarwatsa al’ummar gari da rana tsaka suna harbin kan mai uwa da wabi, sannan su kashe na kashewa sannan su ɗauki na ɗauka, wani lokaci kuma su kan shiga gari salun-alun ba tare da motsi ba suna shiga gida-gida suna ɗaukar mutane.
Yanzu haka ƙauyuka da dama sun koma kufai, duk mutanen ƙauyukan sun gudu zuwa waɗansu manyan garuruwan da ke kusa da su. Yadda matsalar ta fi ban tsoro har da jami’an tsaro a kan kai wa hari a shingen bincike da ke kan hanyoyi, musamman akan hanyoyin da ke kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar da Benin.
A baya-bayan nan waɗansu mahara da ake sa ran mayaƙan Lakurawa ne sun kai hari a wani sansanin jami’an kwastom da ke kan hanyar iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar da Benin a ƙaramar hukumar Bagudo, inda suka halaka biyu daga cikinsu kuma suka cinna wuta a gidajensu.
Wani mazauni garin Kamba, Malam Ali Ibrahim, ya labarta wa Wakilin Blueprint Manhaja cewa, yanzu haka mafi yawancin ƙananan ƙauyukan da ke yankin duk sun gudu zuwa waɗansu manyan garuruwa da ke kusa da su sanadiyyar hare-haren da a ke kai musu kowane dare ana ƙwace shanun da suke noma da su, wanda ya yi sanadiyyar ba za su iya noma ba.
Wani mazauni garin Utono da ke ƙaramar hukumar Ngaski da bai so a bayyana sunansa ba, saboda dalilan tsaro, ya bayyana cewa, ’ƴan bindiga sun ɗora musu harajin Naira miliyan 100, kuma idan ba su biya ba, babu wanda zai yi noma a yankin, wanda ya sanya da yawa hijira daga garin da kuma waɗansu ƙauyukan da ke kusa da su.
Haka zalika, wata mai kama da wannan, a garin Bena da ke ƙaramar hukumar Danko Wasagu da ke iyaka da Jihar Zamfara kuma ɗaya daga cikin yankunan da suka daɗe suna shan wahalar hare-haren ’ƴan bindiga su ma an ɗora musu harajin Naira miliyan 40 ko dai su biya ko kuma ba za su yi noma ba.
Rahotanni daga yankin masarautar Yauri sun bayyana cewa, sama da ƙauyuka 30 ne ’yan bindiga suka watse, wanda kashi 98 na mazauna ƙauyukan manoma ne, kuma sun gudu zuwa waɗansu manyan garuruwa.
Jihar Kebbi dai tana cikin tsaka mai wuya, saboda yanayin hare-haren ya kasu kusan kashi uku, inda a ɓangaren masarautar Zuru masu garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa ne ke addabar su, yankin yamma kuma akwai Fulani da ake sa ran ’yan ƙasar ne ke shiga irin ta Lakurawa suna shiga gida-gida cikin dare suna ƙwace dabbobi, musamman shanu, sai kuma Lakurawa da ke cin karensu ba babbaka, saboda waɗansu bayanai na nuni da cewa, yanzu har mutanen waɗansu ƙauyukan da ke kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar, musamman a ƙaramar hukumar Arewa sun soma sabawa da su, saboda yanzu haka su ke riƙe da ƙauyukan yayin da waɗansu ƙauyukan suka koma kango.
Duk da ya ke dai ba kasafai jami’an tsaro ke kai ɗauki ba ko an kira su yayin da aka kai hari a wani gari ba, amma sau da yawa sukan yi arangama da mayaƙan Lakurawa ko kuma ’yan bindiga kuma su kan yi nasara a kan su. Sau da yawa jami’an tsaro ke kashe Lakurawa, amma ba wai idan an kira su ba, sai dai idan sun haɗu ne da Lakurawan akan hanya, to a nan kam za su tsaya su kare kansu, kamar yadda waɗansu mutanen ƙauyukan da lamarin ya fi shafa suka bayyana.
A baya-bayan nan sojoji sun sami nasarar ƙwato makamai yayin wani artabu da wasu da ake zargin ’yan ta’addan Lakurawa ne a yayin wani sintiri da suka gudanar a ƙaramar hukumar Dandi, inda suka ƙwato makamai da wasu kayayyaki bayan musayar wuta.
Rahotanni sun bayyana cewa, dakarun Runduna ta 1 da ke aiki daga Sansanin Gaba na Kyangakwai sun yi sintiri zuwa yankin Dogon Daji a ranar 14 ga Yuni, inda suka ci karo da ’yan ta’addar. Bayan musayar wuta, maharan sun tsere daga wurin, yayin da sojojin suka ƙwato bututun harba roka (RPG) guda ɗaya, abubuwan fashewa guda uku, babura biyu da wasu kayayyaki da suka bari a baya.
Sai dai rundunar ’yan sandan jihar Kebbi ta sanar da kama waɗansu mutane bakwai kan hanyar garin Illo zuwa Lolo da ake zargi da hannu wajen taimaka wa ’yan ta’adda a daidai jejin Soda bayan samun bayanan sirri.
Bincike ya nuna mutanen sune ke kai-komo wajen sayo wa waɗannan ɓata-garin abinci da sauran hidimomi yayin da su kuma suna can ɓoye a cikin jeji. Waɗanda aka kama dai sun haɗa da Muhammadu Bande, Aliyu Abubakar da Muhammadu Aliyu. Bayan kammala bincike za a tura su kotu, kamar yadda rundunar ta ayyana.
