Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya (IGP), Olatunji Disu, ya haramta wa dukkan jami’an rundunar ’yan sanda ƙirƙira ko wallafa bidiyo, shirye-shiryen kai tsaye (live streams), skit da duk wani nau’in abun ciki a kafafen sada zumunta kamar TikTok, Facebook, Instagram da YouTube ba tare da izinin hukumomi ba.
A wata sanarwa da aka fitar daga Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda da ke Abuja mai kwanan wata 22 ga Yuni, 2026, IGP Disu ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu jami’ai ke amfani da kafafen sada zumunta wajen tallata kansu ko samun kuɗaɗen shiga yayin da suke sanye da kayan aiki ko kuma suna bayyana kansu a matsayin jami’an ’yan sanda.
Sanarwar ta umarci dukkan rundunoni, sashe-sashe da ofisoshin ’yan sanda a faɗin ƙasar nan da su dakatar da irin waɗannan ayyuka nan take.
Sabuwar dokar ta hana jami’ai yin bidiyo ko skit domin nishaɗi, tallata kansu ko neman kuɗi yayin da suke sanye da kayan aikin ’yan sanda ko kuma a cikin harabar ofisoshin rundunar. Haka kuma an hana su amfani da asusun sada zumunta na sirri ko na ɓoye domin harkokin kasuwanci da suka danganci aikinsu.
Haka zalika, an hana jami’an yin tsokaci a bainar jama’a kan bincike, canjin wurin aiki, sauyin mukami, matakan ladabtarwa ko kuma wallafa bayanan sirri da suka shafi ayyukan tsaro, dabarun aiki da tura jami’ai wurare daban-daban.
IGP Disu ya ce irin wannan ɗabi’a na iya lalata martabar rundunar tare da rage amincewar jama’a ga jami’an tsaro. Ya bayyana cewa hakan ya saɓa wa Dokar ’Yan Sanda ta shekarar 2020, ƙa’idojin aikin rundunar, manufofin amfani da kafafen sada zumunta da kuma Dokar Yaki da Laifukan Intanet.
A cewarsa, duk jami’in da aka samu da karya wannan umarni zai fuskanci hukunci mai tsauri wanda ya haɗa da dakatar da aiki, rasa albashi yayin bincike, rage matsayi, kora daga aiki ko ma gurfanar da shi a gaban kotu bisa dokokin laifukan intanet da sauran dokoki masu alaƙa.
Sanarwar ta kuma gabatar da tsarin alhakin shugabanni (vicarious liability), inda aka ce kwamishinonin ’yan sanda, DPOs da sauran masu kula da jami’ai za su iya fuskantar hukunci idan aka tabbatar sun san da irin wannan saɓo amma suka kasa ɗaukar mataki.
An umurci shugabannin rundunonin da su sanya ido kan ayyukan jami’ansu a kafafen sada zumunta tare da kai rahoton duk wanda ya karya dokar.
Hedikwatar rundunar ta bai wa dukkan ofisoshi wa’adin kwanaki bakwai domin sanar da jami’ai wannan umarni da kuma karɓar rubutacciyar shaidar fahimtarsu. Haka kuma kwamishinonin ’yan sanda za su gabatar da rahoton bin umarnin cikin kwanaki 14 ga Mataimakin Sufeto Janar mai kula da ayyuka (DIG Operations).
Bugu da ƙari, IGP Disu ya umurci Hukumar Leken Asiri ta Rundunar (Force Intelligence Bureau) da kuma ɗ-Sƙuad da su fara sa ido kan kafafen sada zumunta domin gano jami’an da suka karya dokar.
Jami’an da ke da asusun ƙirƙirar abun ciki da ke da alaƙa da matsayinsu na ’yan sanda an umurce su da su rufe irin waɗannan asusu ko kuma su cire duk wata alaƙa da rundunar cikin kwanaki 14 tare da gabatar da rahoton bin umarnin.
“Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya cibiya ce ta ladabi da ƙwarewa, kuma nasararta ta ta’allaka ne kan amincewar jama’a da kuma kyawawan ɗabi’un jami’anta. Ba za mu lamunci duk wani abu da zai zubar da mutuncin rundunar ko ya kawo cikas ga ayyukanta ba,” inji IGP Disu.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da amfani da kafafen sada zumunta ke ƙara yaɗuwa tsakanin jami’an tsaro da sauran ma’aikatan gwamnati a faɗin ƙasar nan.
