Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Alhaji Yahaya Umar Bagobiri, jigon ɗan siyasa a jihar Kano ɗan asalin Faruruwa a ƙaramar Hukumar Shanono, ya bayyana cewa haɗin kan al’umma da jami’an tsaro shi ne sirrin samun nasara kan ‘yan bindiga a yankin Arewacin Kano.
Bagobiri ya ce matsalar tsaro ta wuce wuri ɗaya, “Nijeriya ce gaba ɗaya. Nan da can abubuwa na faruwa, sai dai addu’a.”
Ya ce tun a watan Afrilu 2022, da suka ga ta’addanci ya soma shigowa yankin Kano daga yankin Gulbin Karaɗuwa har zuwa cikin Faruruwa, sai suka zauna da masu ruwa da tsaki. “Mun haɗa Dagatai, malaman addini, ‘yan boko da kansiloli. Mun kafa kwamitin tsaro, kuma aka naɗa ni shugaba a matsayina na tsohon ɗan sanda mai ritaya,” in ji shi.
Ya ce kwamitin na da mambobi da suka haɗa da Farfesa MD Muktar a matsayin sakatare, Isyaku Umar tsohon ma’aikacin gwamnati, Limamin Juma’a Malam Badamasi, da sauransu.
“Daga nan muka kafa ƙungiyar ‘yan sa-kai domin su taimaka wa JTF. Domin su ne ‘yan gida da suka san kowane saƙo da lungu,” ya ce.
Bagobiri ya ce sun sayawa ‘yan sa-kai kayan aiki da suka haɗa da kokara da fitilu , da sauran kayan kare kai, sannan aka haɗa su da JTF. Duk da haka, ya ce ‘yan ta’adda sun ci gaba da shigowa suna korar dabbobi da sace kayan mutane, da shiga gida-gida. “Amma muna ta bakin ƙoƙari wajen bai wa al’umma kariya.”
Ya ce ‘yan bindigar sun kashe rayuka kuma sun lahanta mutane da yawa. “Amma ba mu yi ƙasa a guiwa ba. Mun ci gaba da tallafa wa ‘yan sa-kai da JTF har Allah ya sa aka ci ƙarfinsu.” Ya yabawa Kwamishinan ‘Yan Sanda na Kano da Birged Kwamandan Sojoji na Kano, da shugaban rundunar sojin sama bisa haɗin kan da suka bayar.
Bagobiri ya ce sun kafa tsarin samun bayanan sirri tun daga Funtua, Bakori, Malumfashi, da Matazu. “Daga an ce ga ‘yan bindiga sun taso a babura, za a sanar da mu adadinsu. Mu kuma mu sanar da ‘yan sa-kai da JTF su yi musu ƙwanton ɓauna. Har yanzu ƙasar Kano ta gagari ‘yan bindigar tsallakowa.”
Ya ƙara da cewa akwai sansanonin sojoji a wurare daban-daban da ‘yan bindiga ka iya shigowa, kuma ana ba da tsaro sosai.
Ya ce a lokacin da lamarin ya yi tsanani, mutane da dama sun bar garuruwansu saboda fargaba. “Sai shi da Sanata Barau I. Jibrin da sauran masu faɗa a ji na yankin suka tara kuɗi, suka sayi kayan abinci aka raba gida-gida, tare da ba da tallafi iri-iri.”
A cewarsa, yanzu an samu zaman lafiya kashi 80% a yankunan. “Mafi yawan waɗanda suka yi hijira sun koma garuruwansu suna zaune lafiya. Sai kaɗan daga cikin ƙananan abubuwan da ba za a rasa ba.”
Ya ce an kuma kama mutane 14 da ake zargi da ba ‘yan bindiga bayanai, wasu har sun soma riƙe bindiga. “An san kowa, muka kama su muka miƙa su ga hedikwatar ‘yan sanda. Yanzu an saki 9 bayan bincike, 5 na hannu.”
Dangane da damina, Bagobiri ya ce sun umarci manoma da kada su yi shuka mai tsawo da duhu. “Muka ce su shuka riɗi, wake, gyaɗa da sauran amfanin da za a iya ganin mutum daga nesa. Wannan zai hana ‘yan bindiga samun mafaka.”
Alhaji Yahaya Umar Bagobiri ya ce suna ƙoƙarin ganin shugabannin ƙananan hukumomin yankin sun samawa manoma iri mai saurin girma. “Har yanzu muna jiran gwamnati ta samar da irin. Mun kuma kai wa Sanata Barau Jibrin buƙatar haka in sha Allah za a samo irin ɗan wuri akan lokaci ga manoman yanikin.
