Rashin tsaro: Rundunar sojoji za ta ɗauki mutum 28,000 aiki

Spread the love


Rundunar Sojojin Nijeriya ta kammala shirye-shiryen ɗauka da horas da ƙarin sojoji 28,000 domin kara karfafa yaki da matsalolin rashin tsaro da ke addabar sassan kasar.

Babban Hafsan Sojojin Kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 26 ga Yuni 2026, yayin wani taron manema labarai da aka shirya domin karrama Ranar Sojojin Nijeriya (NADCEL 2026).

A cewarsa, rundunar tana fadada tsarinta, tana inganta dabarun tura sojoji zuwa wuraren aiki, tare da amfani da fasahohin zamani domin fuskantar sabbin barazanar tsaro da ke tasowa a Nijeriya.

Janar Shaibu, wanda Babban Jami’in Tsare-tsare da Manufofi na Rundunar Soji, Manjo Janar Bamidele Alabi ya wakilta, ya ce rundunar ta kuduri aniyar hana ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka damar ci gaba da addabar al’umma, tare da tabbatar da cewa dukkan ayyukan soja ana gudanar da su ne bisa dokokin aiki, dokokin jin kai na kasa da kasa, da kuma tanade-tanaden kundin tsarin mulkin ƙasa kan kare haƙƙin ɗan-adam.

Ya bayyana cewa kara daukar ma’aikata ya zama wajibi saboda muhimmancin da isassun sojoji ke da shi wajen tabbatar da ingantaccen aiki a dukkan wuraren da rundunar ke gudanar da ayyuka.

Ya kuma bayyana cewa rundunar ta kafa sabon sansanin horas da sojoji a Amasiri Edda, wanda ya zama cibiyar horaswa ta uku ta Rundunar Sojin Nijeriya.

Ya ce rundunar ta kuma kara karfinta ta hanyar samar da sabbin motocin yaki da kayan aikin soja na zamani, tare da karfafa hadin gwiwa da abokan hulda domin inganta nasarar ayyukanta.

Duk da kalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta, Janar Shaibu ya ce Rundunar Sojin Najeriya ta ci gaba da sauke nauyin da aka ɗora mata na kare ƙasa dak dukkan matsalolin tsaro.

Kazalika, ya ce a halin yanzu sojoji na gudanar da ayyuka a sassa daban-daban na kasar, inda suke ci gaba da raunana kungiyoyin Boko Haram, ISWAP, ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane, kungiyoyin masu neman ballewa da sauran kungiyoyin da ba na gwamnati ba da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron Nijeriya.

By Babaji